Raba wa talakawa kuɗi don rage raɗaɗin cire tallafin mai ba shi ne mafita ba – Gwamnan Kaduna

0
283

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya soki tsarin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta bijiro da shi na raba wa ‘yan Najeriya tallafin rage raɗaɗin cire tallafin mai.

Ita dai gwamnatin ta ce za ta raba wa ‘yan ƙasar miliyan goma sha biyu ne, daga cikin su sama da miliyan 200. Za ta bawa kowane ɗan ƙasa Naira dubu ɗari takwas har tsawon watanni shida.

Sai dai a cewar gwamnan na Kaduna, babu fa’ida a wannan al’amari domin ba zai taimaka kamar yadda ita gwamnatin ke fata ba.

KU KUMA KARANTA: Cire tallafin mai: COEASU ta umarci malamansu da su yi aikin kwanaki biyu a mako

Ya ce ”Abin da muka gano shi ne mu a nan Arewa, kashi 75 cikin 100 na al’ummarmu ba su da asusun ajiya, idan kuma mutum bai da asusun ajiya a banki ta yaya wannan tallafi zai same shi?”

Gwamna Uba Sani, ya ce shi ya sa duk lokacin da aka yi maganar bayar da tallafi a Najeriya sai ka ga ‘yan Kudu ne ke amfana, domin yawancinsu, na da bankunan ajiya, da kuma sani kan yadda za su ci gajiyar tsarin.

Leave a Reply