Ra’ayoyin wasu ‘yan Najeriya mazauna ƙetare game da batun amsar haraji daga hanunsu

0
16
Ra'ayoyin wasu 'yan Najeriya mazauna ƙetare game da batun amsar haraji daga hanunsu

Ra’ayoyin wasu ‘yan Najeriya mazauna ƙetare game da batun amsar haraji daga hanunsu

Chief Olumofin ya ce hakan zai taimaka wajen samar da kudin shiga ga gwamnatin kasar.

Lokuttan da aka yiwa lakabi da ‘Detty December’ lokaci ne da yan Najeriya da dama dake zaune a kasashen waje kan komo kasar su ta haihuwa domin ganawa da yan’uwa da abokan arziki. Lokaci ne da kan kama daga tsakiyar watan Disamba har zuwa cikin sabuwar shekara da ake gudanar da bukuwa da kan tattaro yan Najeriya dake zaune a kasashen duniya dabam dabam.

KU KUMA KARANTA:Kenya ta amince da baiwa ‘yan Afrika izinin shiga ƙasar kyauta

Da yake bayyana ra’ayin sa akan batun, wani mazaunin Landan, Abdussamad Aminu Galadima, ya ce, baya tunanin wannan shawara ce mai muhimmanci ga gwamnatin Najeriya, saboda yan Najeriyar dake zuwa gida hutun kirsimeti daga kasashen waje, kudin su suke kashewa su hawo jirgi su zo gida, sannan duk kudin da za su kashe a cikin kasar, a kasar za su tsaya, don haka ko a nan ma an taimakawa tattalin arzikin ta. Ya kara da cewa, karbar haraji ba abinda zai haifar illa ya hana wasu mazauna kasashen waje zuwa gida.

Shima Salim Abubakar Abacha cewa yayi ‘maganar gaskiya wannan shawarar banza ce kawai, kasancewar yan Najeriya mazauna kasashen waje da kan koma gida a lokuttan bukukuwan Kirsimeti, suna yin wasu hidimomin na kudi a kasar, don haka don me za su biya wani haraji?’ A ganin shi tafiyar ma da suke yi zuwa gida shi kan shi ai karawa kasar arziki ne.

Da dama dai ina ganin ace wai mazauna kasashen waje su biya harajin $500 idan sun dawo gida hutu, tamkar Kura da shan duka ne, gardi da kwace kudi, saboda mutum zai yi fadi tashi ya fita zuwa wata kasa yayi aiki domin neman rufin asiri, sannan kuma ace ya biya kasa wani haraji, suka ce hakan ko da wasa bai dace ba.

Leave a Reply