Raɗaɗin rashin iyali na ba zai taɓa rabuwa da ni ba – Tijjani Babangida

0
56
Raɗaɗin rashin iyali na ba zai taɓa rabuwa da ni ba - Tijjani Babangida

Raɗaɗin rashin iyali na ba zai taɓa rabuwa da ni ba – Tijjani Babangida

Daga Ibraheem El-Tafseer

Tsohon ɗan wasan Super Eagles, Tijjani Babangida, ya bayyana damuwarsa kan yadda ya rasa iyalinsa a wani hatsarin mota da ya faru farkon shekarar nan.

Hatsarin ya faru ne a ranar 9 ga Mayu, 2024, a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Zaria, yayin da Babangida ke tafiya tare da ƙaninsa Ibrahim, matarsa, ɗansu mai shekara ɗaya Fadil, da kuma wata yar aiki.

Hatsarin ya yi sanadin rasuwar Ibrahim, wanda ya mutu nan take, sai kuma Fadil, wanda ya rasu bayan kwanaki.

Matarsa ta ji munanan raunuka, har ta rasa ido ɗaya kuma aka yi mata aikin gyaran fuska, inda ƴar aikin kuma ta ji rauni a ƙafarta.

A cikin wani shirin bidiyo mai cike da tausayi da Ajax Amsterdam, tsohuwar ƙungiyarsa, suka fitar a jiya Alhamis, Babangida ya bayyana irin raɗaɗin da wannan haɗari ya jawo masa da kuma yadda ya bar alama mai ɗorewa a rayuwarsa.

KU KUMA KARANTA: Hatsarin mota a Yobe ya ci rayukan mutane 12

“Ina ganin zan rayu da wannan raɗaɗin har karshen rayuwata,” in ji Babangida. “Da wuya mutum ya manta ya ci gaba da rayuwa bayan ya rasa dukkan iyalinsa ba zato ba tsammani. Wannan shi ne karon farko da nake magana kan hatsarin saboda ya yi mini ciwo har na kasa magana.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here