Paul Alexander, majinyacin da ke numfashi da huhun ƙarfe ya mutu

0
168

Paul Alexander ya rasu ranar Litinin yana da shekaru 78, a cewar wata sanarwa da ɗan’uwansa, Philip Alexander, ya fitar ta kafar sada zumunta.

Paul Alexander, wanda ya mutu yana da shekaru 78 a duniya ya kamu da cutar shan inna yana da shekaru 6, ya kuma rayu na tsawon shekaru 70 yana numfashi ta wajen amfani da injin numfashi. Duk da haka, ya samu damar samun digiri na shari’a, ya kuma rubuta littafi.

Bayan da cutar shan inna ta shanye shi yana a shekara 6, lamarin ya tilastawa Paul Alexander dogara ga amfani da huhun ƙarfe.

Rayuwa a cikin huhun ƙarfe sakamakon kamuwa da cutar shan inna bai hana Alexander zuwa jami’a ba, ya samu digiri na shari’a da kuma aikin lauya fiye da shekaru 30 da suka shige. Lokacin da yake yaro, ya koya wa kansa numfashi na tsawon mintuna da sa’o’i a lokaci guda, duk da haka ya zama dole ya yi amfani da injin a kowace rana ta rayuwarsa.

Ya kasance ɗaya daga cikin mutane kaɗan da su ka rage a Amurka da ke zaune a cikin huhun ƙarfe. Kuma a cikin makonnin ƙarshe na rayuwarsa, ya nuna wa mabiyansa na TikTok yadda ya ke rayuwarsa da taimakon injin.

Ba a bayyana dalilin mutuwarsa a hukumance ba. Amma Alexander ya ɗan jima yana asibiti don ya kamu da cutar Covid-19 a watan Fabrairu, a cewar shafinsa na TikTok. Bayan ya koma gida, Alexander ya yi fama da rashin cin abinci da shan ruwa yayin da yake murmurewa daga cutar, wacce ke auka wa huhu kuma tana iya zama haɗari musamman ga mutanen da suka tsufa kuma suna da matsalar numfashi.

Alexander ya kamu da cutar shan inna a shekara ta 1952, a cewar littafinsa, “Three Minutes for a Dog: My Life in an Iron Lung.” wanda ya rubuta ta hanyar sanya Alƙalami ko fensir a bakinsa. Nan take likitocin asibitin Parkland da ke Dallas suka sanya shi cikin huhun ƙarfe domin ya samu yin numfashi.

Lokacin da yake cikin injin, Alexander yakan buƙaci taimakon wasu don ayyuka na yau da kullum kamar ci da sha.

KU KUMA KARANTA:Hukumar kwastom ta kama muggan ƙwayoyi da makamai a tashar jiragen ruwa na Legas

Alexander ya ƙaddamar da shafin TikTok ɗinsa a watan Janairu, kuma, tare da taimakon wasu, ya fara ƙirƙirar bidiyo game da rayuwarsa.

A cikin wani bidiyo, Alexander yayi cikakken bayani game da ƙalubalen tunani na rayuwa a cikin huhun ƙarfe.

“Akwai kaɗaici,” in ji shi “Wani lokaci ina cikin matsananciyar damuwa saboda ba zan ma iya taɓa wani ba, hannayena ba sa motsowa.”

Alexander ya faɗa a cikin bidiyon cewa ya shafe shekaru da dama yana samun saƙonnin imel da wasiƙu daga mutanen da ke fama da damuwa da kaɗaici, ya kuma ba su shawarwari.

Leave a Reply