Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙi na zamanl, Farfesa Isa Pantami, ya buƙaci masu hannu da shuni da su taimakawa marasa galihu a cikin al’umma don rage musu yanayin rayuwarsu.
Malam Pantami ya yi wannan roƙo ne a lokacin da yake jagorantar ɗaurin auren Muhammad Oyanki, ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Doma ta Arewa a majalisar dokokin jihar Nasarawa, da matarsa, Ruƙaiya Shehu, a ranar Juma’a a masallacin Annur, Abuja.
Tsohon ministan kuma malamin addinin Islama sun ɗaura auren ne bayan bayyana sadaki Naira 100,000 tare da gabatar da takardar shaidar likita na lafiyarsu.
Ya kuma buƙaci ’yan Najeriya da su yi addu’a sosai domin Allah ya shiga cikin ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.
KU KUMA KARANTA: NEMA ta ba da tallafin kayan agaji ga mutane dubu 23 a Nijar
Ya yi addu’ar Allah ya albarkaci auran sabbin ma’auratan.
Malamin ya taya Oyanki da matarsa murna, inda ya yi musu gargaɗi da su riƙa nuna soyayya, haƙuri, fahimta da haƙuri da sauran kyawawan ɗabi’u don samun nasarar aurensu.
Daga baya angon ya godewa Allah da ya sa burinsu ya zama gaskiya.
Ɗan majalisar ya godewa duk waɗanda suka halarci daurin auren, ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan su da rahama a wuraren da suka nufa, ya kuma saka musu da alheri.
Baya ga haka, Oyanki ya tabbatar wa ‘yan majalisarsa nagartaccen wakilci mai inganci a majalisar dokokin jihar. Abel Bala mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa ne ya jagoranci sauran takwarorinsa wajen halartar taron.
Mawaƙan yabo sun nishaɗantar da baƙi a wajen taron.
[…] KU KUMA KARANTA: Pantami ya yi ƙira da a tallafawa talakawan Najeriya, don rage musu raɗaɗi […]