NUJ Yobe ta yi Allah-wadai da rahoton ƙarya na kashe-kashe da jaridar PUNCH ta yi a jihar, ta yi kira da su gaggauta ba da haƙuri
Ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa reshen jihar Yobe, NUJ, ta yi kakkausar suka ga wani rahoto da jaridar Punch ta buga na yau yau Alhamis (11/09/2025), inda ta yi zargin cewa an kai hari a al’ummar garin Mafa ta jihar Yobe, inda ta bayyana rahoton a matsayin ƙarya, yaudara, kuma ƙage ne gaba ɗaya.
A wata sanarwar manema labarai da kungiyar ta NUJ Yobe ta fitar a ranar Alhamis, 11 ga Satumba, 2025, ta bayyana kaɗuwarta kan abin da ta kira aikin jarida na rashin gaskiya da riƙon amana da Punch ta yi, inda ta dage cewa babu wani abu makamancin haka da ya faru a Mafa ko kuma a cikin jihar kamar yadda aka ruwaito.
Sanarwar mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar ta NUJ, Kwamared Rajab Ismail Mohammed, ya yi gargaɗin cewa yaɗa bayanan da ba a tabbatar da su ba na iya haifar da firgici da yaɗa labaran ƙarya, musamman a jihar da ta yi ƙoƙarin maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Tun daga nan ƙungiyar ta umurci kwamitin ɗa’a da ladabtarwa da ya gayyaci wakilin jaridar Punch, Mista Kagana Amshi, domin gudanar da bincike kan rahoton da ya yi na ƙarya.
Ƙungiyar ta jaddada buƙatar ‘yan jarida su kiyaye ƙa’idojin gaskiya, daidaito, da sanin makamar aiki, inda ta buƙaci masu aikin yaɗa labarai da su riƙa tantance rahotanni sosai kafin a buga su.

Ƙungiyar ta NUJ Yobe ta yi kira ga Jaridar Punch da ta gaggauta janye rahoton na ƙarya sannan ta bayar da uzuri ga gwamnati da al’ummar Yobe musamman al’ummar Mafa da ta shiga cikin damuwa ba tare da wata matsala ba.
Ƙungiyar ta kuma shawarci jama’a da su yi watsi da wannan labarin sannan su dogara da ingantattun majiyoyin labarai masu inganci don samun ingantattun bayanai.









