NOA ta bankaɗo badaƙalar jami’o’i da bankuna na zaluntar ɗalibai kan bashin ilimi
Daga Shafa’atu Dauda Kano
Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA) ta bankado wata babbar badakala da ta shafi hadin gwiwar wasu jami’o’i da bankuna wajen tauye hakkokin dalibai a shirin bayar da bashin karatu na gwamnatin tarayya (NELFUND).
Binciken da jami’an Community Orientation and Mobilisation Officers (COMO) na NOA suka gudanar ya gano cewa wasu jami’an makarantu da bankuna na hada baki wajen ɓoye bayanai, jinkirta sakin kudade, ko ma karɓar su ba tare da sani ko amincewar daliban da suka cancanta ba.
Wannan matsala ta janyo cikas ga samun tallafin ga dalibai da ke da haƙƙi a kai, tare da jefa su cikin tsananin ƙuncin rayuwa da barazanar dakatar da karatu.
A cewar wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Sadarwa da Watsa Labarai na NOA, Paul Odenyi, ya fitar a ranar Lahadi, hukumar ta tabbatar da cewa ana gudanar da wadannan ayyuka ne ba tare da bin ka’idoji ba, kuma hakan yana karya dokokin da suka kafa asusun NELFUND.
KU KUMA KARANTA:Muna ƙira ga gwamnatin Kano da ta samar mana da Asibiti – Al’ummar Unguwar Magashi
Daraktan Gabaɗaya na NOA, Malam Lanre Issa-Onilu, ya bayyana abubuwan da aka gano yayin wata ganawa da Shugaban Hukumar NELFUND, Mista Akintunde Sawyerr. A cewarsa, akwai jami’an makarantu da ke boye bayanai ko bayar da bayanan ƙarya domin rage adadin daliban da za su amfana da tallafin. Bankuna kuma na taka rawa wajen hana dalibai samun cikakken bayani game da sharuddan da hanyoyin neman bashin.
A wani bangare na matakan da aka fara ɗauka, NELFUND ta bayyana aniyar ta na daukar matakin doka kan duk wata cibiyar ilimi da aka samu da laifi, inda Mista Sawyerr ya jaddada cewa wannan danyen aiki ba wai kawai rashin gaskiya ba ne, har ma da take dokokin NELFUND.
Hukumar NOA ta bukaci gwamnatin tarayya da hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta ɗaukar matakai masu tsauri domin dakile wannan dambarwa. Haka kuma, ta shawarci dalibai da su rika kai rahoton duk wani rashin adalci da suke fuskanta wajen neman bashin karatu.
NOA ta jaddada aniyarta na ci gaba da bin diddigin lamarin domin kare haƙƙin ɗalibai da tabbatar da gaskiya da adalci a harkar ilimi a Najeriya.
An bayyana cewa bincike zai ci gaba, tare da sa ran ɗaukar karin matakai a cikin makonni masu zuwa.