NNPC ta samu ribar Naira biliyan 539 a watan Agustan 2025

0
130
NNPC ta samu ribar Naira biliyan 539 a watan Agustan 2025

NNPC ta samu ribar Naira biliyan 539 a watan Agustan 2025

Daga Jameel Lawan Yakasai

Kamfanin Man Fetur na Ƙasa NNPCL ya bayyana cewa ribar da ya samu bayan haraji a watan Agusta 2025 ta kai Naira biliyan 539, yayin da jimillar kuɗaɗen shigar sa ya kai Naira tiriliyan 4.65.

Haka kuma, daga Janairu zuwa Yuli, kamfanin ya biya haraji da ya haura Naira tiriliyan 8.86.

Rahoton ya nuna cewa NNPC ta samar da ganga miliyan 1 da dubu 665 na danyen mai da kuma cubic feet miliyan 6,949 na iskar gas a kullum, abin da ya nuna ci gaba a fannin samar da makamashi duk da ƙalubalen da ake fuskanta a sashen.

KU KUMA KARANTA: Ribar da muke samu ta ragu da kashi 79% a watan Yuli – NNPC

Haka kuma, rahoton ya nuna yadda gidauniyar NNPC Foundation ke taka rawa wajen bunƙasa al’umma, inda ta shirya horo kan ilimin sarrafa kuɗi ga matasa da ɗaliba masu yiwa kasa hidima (NYSC) fiye da 60,000 a jihohi 36 da Abuja, da hakan ya kawo jumullar matasan da gaidauniyar ta horas zuwa dubu 930 da 614.

Leave a Reply