NLC ta caccaki gwamnatin tarayya kan ƙara farashin man fetur

0
50
NLC ta caccaki gwamnatin tarayya kan ƙara farashin man fetur

NLC ta caccaki gwamnatin tarayya kan ƙara farashin man fetur

Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta caccaki Gwamnatin Bola Tinubu kan ƙarin farashin litar man fetur da aka yi a ƙasar.

Shugaban NLC na ƙasa, Kwamared Joe Ajaero ne ya bayyana kaɗuwar ƙungiyar cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin jiya Larabar.

A cikin sanarwar,  Kwamared Ajaero ya ce “da alama dai babu abin da wannan gwamnatin ta sani face ƙara kuɗin man fetur ba tare da tuntuɓar kowa ba, ba kuma tare da an wadata ’yan ƙasar da hanyoyin rage raɗaɗi ba.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa tsame hannun dillanci da kamfanin mai na ƙasa NNPCL ya yi tsakanin ’yan kasuwa da matatar Ɗangote abin dubawa ne.

“Ya kamata gwamnati ta sake nazari ta kuma gabatar mana shirin da take yi na bunƙasa tattalin arzikin Najeriya, da ci gaban ƙasa maimakon ɗaukar matakan da ba su wani tasiri sai dagula lamurra,” in ji NLC.

KU KUMA KARANTA: Ƙarin farashin man fetur ya karya darajar mafi ƙarancin albashi na dubu 70 — NLC

A ranar Laraba ne aka wayi gari kamfani NNPCL ya kara farashin man a karo a biyu cikin wata guda.

A Abuja, babban birnin ƙasar, sabon farashin lita ɗaya ya fara daga naira 1,030, sabanin yadda ake sayar da shi a baya kan naira 897.

A bayanan sabon farashin da NNPCL ya fitar, za a riƙa sayar da duk litar man fetur kan Naira 1,025 a gidajen mansa da ke Kudu maso Yamma sannan a riƙa sayarwa kan Naira 1,045 a Kudu maso Gabashin Najeriya.

Haka kuma, sabon farashin ya nuna litar man fetur ta koma Naira 1,075 a Kudu maso Kudu da Arewa maso Gabas sannan a riƙa sayarwa kan Naira 1,070 a Arewa maso Yamma da kuma Naira 1,030 a Arewa ta Tsakiya.

Tun a watan Satumba ne NNPCL ya ƙara farashin litar man daga N617 zuwa N897 gabanin ya fara sayen man daga Ɗangote, yana mai cewa yana fama da ƙarancin kuɗi.

Leave a Reply