NLC ta ƙira taron gaggawa bayan gwamnati ta jingine batun ƙarin albashi

NLC ta ƙira taron gaggawa bayan gwamnati ta jingine batun ƙarin albashi

NLC ta ƙira taron gaggawa bayan gwamnati ta jingine batun ƙarin albashi

Daga Muhammad Kukuri 

Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta ƙira taron gaggawa bayan Majalisar Zartaswa ta Tarayya ta jingine maganar karin mafi karancin albashi.

KƘungiyoyin ƙwadagon za su yi zaman ne da misalin karfe 10 na safiyar Laraba a Abuja, bayan matakin da Gwamnatin Tarayya ta jingine wasikar da ta fitar da farko kan karin mafi karancin albashin domin ba wa Shugaba Tinubu damar faɗaɗa tuntuɓar ɓangarorin da lamarin ya shafa.

Sun sanar da haka ne bayan Ministan Yada Labari da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, ya sanar bayan taron Majalisar Zartaswa a ranar Talata cewa batun karin albashin ne kawai ba a tattauna a zaman da aka cimma matsaya kan abubuwa 39 da ke kunshe cikin ajandar taron ba.

Ministan ya bayyana cewa kafin zaman an karɓi rahoton kwamitin karin albashin da ya kunshi matakan gwamnati uku da kungiyar kwadago da kuma kamfanoni masu zaman kansu.

KU KUMA KARANTA: Majalisar Zartaswa ta jingine batun ƙarin mafi ƙarancin albashi

Sai dai, a cewarsa, Majalisar Zartaswa ta jingine aiwatar da umarnin karin mafi karancin albashin ne saboda al’amarin ya shafi duk bangarorin — gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi, kamfanoni masu zaman kansu da ’yan kwadago.

A cewarsa a yi hakan ne domin Shugaba Bola Tinubu ya kara tuntubar masu ruwa da tsaki kafin mika lamarin ga Majalisar Dokoki ta Kasa.

Bayan nan ne wani jigon a ƙungiyar NLC ya tabbatar wa Aminiya a daren Talata cewa shuagabancin kungiyoyin zai yi zaman gaggawa domin cimma matsaya kafin shugaban kasa ya tuntube su yi kan lamarin.

“Duk da cewa mun riga mun yanke shawara, amma za mu sake zama ranar Laraba da safe domin sake duba lamarin kafin su (gwamnati) tuntube mu.

“Zaman na da muhimmanci,” inji babban jami’in na ƙungiyar ƙwadago.

A farkon watan nan na Yuni ne ƙungiyoyin kwadago suka shiga yajin aikin kwana biyu da ya tsayar da harkoki cak a Najeriya.

Sun yi yajin aikin ne domin neman ƙarin mafi ƙarancin albashin da har yanzu ake ci gaba da kai ruwa rana tsakaninsu da ɓangaren gwamnati.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *