NIMET ta yi hasashen ambaliyar ruwa a Kano

0
73

NIMET ta yi hasashen ambaliyar ruwa a Kano

Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya NIMET ta gargaɗi al’ummar Jihar Kano kan yiwuwar samun ambaliyar ruwa a ƙananan hukumomi 14 daga cikin 44 da ke faɗin jihar.

Kodinetan Hukumar NIMET na Kano da Jigawa, Dokta Nuradeen Abdullahi ne ya bayyana haka a wani taron haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki a harkar hasashen yanayi da kuma hasashen ambaliyar ruwa na shekara-shekara a Kano.

Abdullahi ya bayyana ƙananan hukumomin da ke fuskantar wannan barazana da suka haɗa da Rimin Gado, Tofa, Kabo, Madobi, Garum Malam, Bebeji, Rano, Dawakin Kudu, Warawa, Wudil, Sumaila, Ajingi, Kura da Dala.

Sai dai ya ce akwai ƙananan hukumomi biyar da suka haɗa da Karaye, Takai, Bunkure, Dawakin Tofa da Makoɗa waɗanda ake fargabar za su shiga cikin sahun masu haɗarin samun ambaliya.

KU KUMA KARANTA: Ɗaruruwan mutane sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Afghanistan — Taliban

Abdullahi ya ce, sauran ƙananan hukumomi 25 da suka haɗa da: Doguwa, Tudun Wada, Kibiya, Garko, Albasu, Gaya, Ƙiru, Rogo, Gwarzo, Shanono, Tsanyawa, Ɓagwai, Bichi, Ƙunchi, Ɗanbatta, Minjibir, Gabasawa, Gwale, Fagge, Nassarawa, Kano Municipal, Tarauni, Ungogo, Kumbotso da Gezawa – ba su da wata fargaba a yanzu.

Ya ce, taron an yi shi ne don shirin matakai mafi kyawun hanyoyin da za a bi don daƙile afkuwar ambaliya a faɗin jihar.

Ya ce, taron wanda aka yi tare da haɗin gwiwar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA) ya zama dole domin tunatar da masu ruwa da tsaki nauyin da ya rataya a wuyansu dangane da illar sauyin yanayi da kuma iftila’in da zai auka wa muhalli.

Abdullahi ya bayyana mata da yara ƙanana a matsayin waɗanda suka fi fama da matsalar a lokacin damina, sannan ya buƙaci jama’a a yankunan da ke da haɗarin samun ambaliyar ruwan da su ɗauki matakan kariya kafin sauƙar damina.

Leave a Reply