Nijar za ta koma amfani da tashoshin jiragen ruwan ƙasashen Libiya da Aljeriya

0
118

Nijar ta bayyana aniyarta na ƙarfafa cinikayya da ƙasashe makwabtanta irin su Aljeriya da Libiya, ta yadda za ta yi amfani da tashoshin jiragen ruwan ƙasashen domin shigo da kayayyaki daga ƙetare ko kuma fitar da kayan ƙasar.

Aniyar da gwamnatin ta Nijar ta ƙudiri yi na zuwa ne kwanaki bayan da ƙasar taƙi amincewa tare da ƙaurace wa shigo da kaya ta tashar jiragen ruwan Kwatonou da ke zama mafi kusa ga ƙasar.

Sai dai ƙungiyoyin ‘yan kasuwa sun yi lale marhabin da shirin, yayin da masana tattalin arziki ke ganin akwai buƙatar yin taka tsan-tsan a cikin lamarin.

Ƙungiyar Ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta sanya wa Nijar takunkumin karya tattalin arziki, sakamakon juyin mulki a ranar 26 ga watan Yulin shekarar da ta gabata da sojoji suka yi, wanda ya yi sanadiyyar rashin shigo da kayayyaki wajen amfani da tashar jiragen ruwan Kwatonou ta jamhuriyar Benin.

KU KUMA KARANTA: ‘Ƙawancen Nijar, Mali da Burkina Faso zai zama na har abada’

Saboda haka gwamnatin Nijar ta duƙufa wajen samo sabbin hanyoyin da zasu sauƙaƙa shigo da kaya a cikin ƙasar ko fita da su zuwa ƙasashen waje.

Gwamnatin mulkin sojoji a Nijar ta sanar da shirin soma amfani da tashoshin ruwan ƙasashen Aljeriya da Libiya, domin shigo da kayayyaki cikin ƙasar.

Alhaji Habou Ali shine shugaban ‘yan kasuwa na ƙasar ta Nijar, ya bayyana jin daɗinsu tare da yin lale marhabin akan wannan sabon shirin da gwamnatin ta ɓullo da shi.

Sai dai yayin da ƙungiyoyin ‘yan kasuwa ke murnar wannan shirin, masanin tattalin arziki, Aminu Ibrahim, na ganin akwai buƙatar gwamnatin Nijar tayi taka tsan-tsan akan wannan lamarin, saboda akwai matsalar ‘yan ta’adda da ake fama da su.

Ibrahim ya ce dole ne sai an ɗauki mataki ƙwaƙƙwara wanda zai tabbatar da ɗaurewar alaƙar.

Gwamnatin ƙasar Nijar ta tura wata tawaga ƙarƙashin jagorancin Ministan Harakokin Wajen ƙasar Nijar zuwa ƙasar Libiya, inda suka tattauna da takwaran aikinsa a ƙasar da nufin inganta alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu da ke makwabtaka da juna.

Leave a Reply