Daga Ibraheem El-Tafseer
Niamey, babban birnin Jamhuriyar Nijar da kuma sauran wasu manyan birane kamar Maraɗi da Zinder sun fara fuskantar katsewar wutar lantarki.
Mutane na samun wutar lantarki ne na tsawon kimanin sa’a ɗaya a wani lokaci daga nan sai a ɗauke tsawon sa’a huɗu ko biyar ba tare da an sake kawowa ba.
Wakiliyar BBC ta ce tsarin bayar da lantarki a babban birnin ƙasar ya koma zuwa bai wa wani ɓangare, a kuma kashe wa wani ɓangare a lokaci guda.
Kamfanin sarrafa lantarki na Nijar (Nigelec) ya ce matsalar na faruwa ne sakamakon katsewar lantarkin da ake samu daga Najeriya. Ƙasar dai wadda shugabanta Bola Tinubu ke jagorantar ƙungiyar Ecowas na ɗaukar wannan mataki ne a wani ɓangare na takunkuman da ƙungiyar ƙasashen ta Afirka ta Yamma ta ƙaƙaba wa Nijar saboda juyin mulkin da sojoji suka yi.
KU KUMA KARANTA: Sojojin Nijar na zargin Faransa na shirin kai hari don kuɓutar da Bazoum
Gwamnatin Najeriya dai ba ta tabbatar da iƙirari ko musanta shi ba zuwa yanzu.
Sai dai, majiyoyi daga Abuja sun ce hukumomin ƙasar sun katse wasu layukan wutar lantarki zuwa Jamhuriyar Nijar, ba tare da yin cikakken bayani ba.
Najeriya, ita ce ƙasa mafi samar da lantarki ga Jamhuriyar Nijar.
Gwamnatin mulkin sojin Nijar dai ta sanar da buɗe kan iyakokin ƙasar da maƙwabtanta biyar, mako guda bayan kifar da gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum.
Manyan ƙasashen duniya da ƙungiyoyi da dama sun yi Allah-wadai da juyin mulkin, sannan ana fargabar ɓarkewar rikice a yankin Sahel sakamakon ƙwace ikon.
Cikin wata sanarwa da kakakin sojojin Kanal Manjo Amadu Abdurahamane ya karanta a gidan talbijin na ƙasar ya ce ”daga ranar 1 ga watan Agusta, an buɗe iyakokin ƙasar da ƙasashen Algeriya da Burkina Faso da Mali da Libya da kuma Chadi”.
Sojojin sun sanar da rufe kan iyakokin ne a makon jiya, daidai lokacin da suka sanar da kifar da gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum.
Kan iyakokin da aka sanar da buɗewa galibi, yankunan hamada ne masu nisa.
To sai dai har yanzu manyan hanyoyin hulɗar kasuwancin ƙasar na ci gaba da zama a rufe saboda takunkuman da ƙungiyar Ecowas ta sanya wa Nijar.
Juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar shi ne na bakwai da aka samu cikin ƙasa da shekara uku a yankin Afirka ta Yamma, inda wasu ƙasashen da aka samu juyin mulkin suka dunƙule waje guda domin nuna adawa da matakin da sauran ƙasashen yankin 15 ke yunƙurin ɗauka a kan Nijar.
[…] KU KUMA KARANTA: Nijar ta shiga matsalar lantarki bayan katsewa daga Najeriya […]
[…] KU KUMA KARANTA: Nijar ta shiga matsalar lantarki bayan katsewa daga Najeriya […]