Nijar ta sake buɗe iyakarta da Najeriya

0
143

Daga Ibraheem El-Tafseer

Jamhuriyar Nijar ta sake buɗe kan iyakarta da Najeriya a yankunan Diffa da Tahoua da Maraɗi da Dosso.

An rufe iyakar ƙasar da ke tsakanin maƙwabtan biyu biyo bayan juyin mulkin da aka yi a ranar 26 ga watan Yuli da kuma takunkumin da ƙungiyar ECOWAS ta ƙaƙaba mata.

A wani saƙon rediyo da aka watsa a shafukan sada zumunta, a ranar Alhamis, ma’aikatar harkokin cikin gida ta Jamhuriyar Nijar ta umurci gwamnonin waɗannan yankuna na kan iyaka da su ba da izinin sake buɗe aiki da ƙarfe 12:00 na dare.

Ma’aikatar ta kuma umurci gwamnonin da abin ya shafa da su ƙarfafa tsaro a kan iyakokin ƙasar.

KU KUMA KARANTA:Shugaba Tinubu ya ba da umarnin buɗe iyakokin Najeriya da Nijar nan-take

An buɗe iyakokin Najeriya makonnin da suka gabata bayan ɗage takunkumin da ƙungiyar ECOWAS ta ƙaƙaba wa ƙasar a wani taro da aka yi a Abuja, amma Nijar ba ta mayar da martani ba nan take.

Sai dai kuma har yanzu kan iyakar Nijar da maƙwabciyar Benin na nan a rufe a ɓangaren Nijar duk da gaggawar aiwatar da umarnin ECOWAS da hukumomin Benin suka yi.

Hukumomin riƙon ƙwaryar Nijar sun bayar da dalilai na tsaro a matsayin dalilin rashin buɗe kan iyaka da maƙwabtanta da ke Kudu.

Leave a Reply