No menu items!

Sample Page Title

Date:

Kasar Nijar ta dakatar da duk wata haɗin gwiwa da ƙungiyar ƙasashe masu amfani da harshen Faransanci (OIF), kamar yadda shugabannin sojojinta suka bayyana, yayin da ta ci gaba da yanke alaƙa da ƙasar da ta yi mata mulkin mallaka na Faransa.

Kungiyar mai mambobi 88 “Faransa na amfani da ita a matsayin makami don kare muradun Faransa”, in ji mai magana da yawun gwamnatin mulkin Nijar a jawabin da ya yi a gidan talabijin na ƙasar da yammacin jiya Lahadi.

A watan Yuli ne sojoji suka ƙwace juyin mulki a Nijar, lamarin da Faransa da sauran ƙawayenta na Yammacin Duniya suka yi Allah wadai da shi.

Nan da nan kuma gwamnatin mulkin sojin ta kori dakarun Faransa daga ƙasar, waɗanda suke taimakon ƙasar wajen yaƙi da masu tsattsauran ra’ayin da suka shafe kusan shekara 10 suna ta da rikici a ƙasar.

KU KUMA KARANTA: Faransa ta rufe ofishin jakadancinta da ke Nijar

Tuni Ƙungiyar OIF ma ta dakatar da mafi yawan ayyukan haɗin gwiwarta da Nijar a makon da ya wuce saboda juyin mulkin, amma ta ce za ta ci gaba da aiwatar da waɗannan shirye-shiryen “da kai tsaye suke shafar al’umma, da kuma masu ƙoƙarin ganin an dawo da dimokuraɗiyya.”

Manufar ƙungiyar ita ce inganta harshen Faransanci da tallafawa zaman lafiya da dimokuraɗiyya, da ƙarfafa ilimi da ci gaba a ƙasashen da ke amfani da harshen Faransanci a duniya, waɗanda yawancinsu tsoffin ƙasashen Faransa ne.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...