Shugaban mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ya ce ƙasarsa da Mali da kuma Burkina Faso za su samar da kuɗin bai-ɗaya domin ƙarfafa tattalin arziki da ci-gabansu.
Janar Abdourahamane Tiani a gidan talbijin na RTS ranar kahadi da maraice.
Sai dai bai yi cikakken bayani kan lokaci da kuma tsarin samar da kuɗin ba, ko da yake ya ce matakin na ɗaya daga cikin dalilan da suka sa ya kai ziyara ƙasashen biyu kwanakin baya.
“Baya ga ƙarfafa harkokin tsaro, dole kawancenmu ya samu tagomashi ta fuskar siyasa da sha’anin kuɗi,” in ji shi.
KU KUMA KARANTA: An bayar da shawarar kafa tarayyar ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso
A halin yanzu dai ƙasashe takwas a Yammacin Afirka, ciki har da Nijar da Mali da Burkina Faso, suna yin amfani da CFA, kuɗin da Faransa ta kakaɓa musu tun zamanin mulkin-mallaka abin da mazauna yankin suke matukar adawa da shi.
Dama dai tuni ƙasashen uku suka ƙafa ƙungiyar kawance ta Alliance of Sahel States (AES) da zummar tunkarar matsalolin tsaron da ke addabarsu da kuma far wa duk wata ƙasa da ta taba ɗaya daga cikinsu.
Haka kuma a farkon watan nan ministocin ƙasashen wajen Burkina Faso da Mali da Nijar sun bayar da shawarar ƙirƙiro tarayyar ƙasashen uku a wani ɓangare na haɗa kan ƙasashen don su zama a dunƙule wuri ɗaya.
Ƙasashen uku, waɗanda suke ƙarƙashin mulkin soji, sun zare kansu daga cikin ƙungiyar ƙasashen G5 Sahel wadda ke haɗa gwiwa da Faransa domin tabbatar da tsaro a yankin Sahel.
Kazalika sun gargaɗi ƙungiyar ECOWAS da ta guji yunkurin amfani da ƙarfin soji a kan Nijar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum a watan Julin da ya gabata.