Nijar da Burkina Faso sun janye daga ƙawancen G5 Sahel na Faransa kan yaƙi da ta’addanci

0
216

Shugabannin rundunonin sojin Burkina Faso da Nijar a ranar Asabar sun ce sun janye daga ƙawancen ƙungiyar G5 Sahel ta ƙasashe biyar da ke yaƙi da masu tayar da kayar baya a yankin Sahel, lamarin da zai haifar da gagarumin koma-baya kan yaƙi da ta’addanci a yankin.

Ƙungiyar ta G5 Sahel, wadda aka kafa a 2014, ba ta taka rawar gani sosai ba, inda a bara Mali ta fice daga cikinta bayan sojoji sun yi juyin mulki a ƙasar.

A shekarar 2017 ne shugabannin ƙasashen biyar tare da goyon bayan Faransa suka amince su tura tawaga ɗaya ta jami’an tsaro na haɗin gwiwa domin fatattakar ‘yan ta’adda a yankin, amma yanzu sojojin da suka yi juyin mulki a Burkina da Nijar da Mali dukkansu sun zargi Faransa da yin shisshigi a cikin lamarin bayan da ta tura karin dakarunta yankin na Sahel.

Burkina da Nijar “sun yanke shawarar cin gashin kansu inda suka janye daga ƙungiyar G5 Sahel, ciki har da ɗauke dakarunsu” daga ranar 29 ga watan Nuwamba, kamar yadda ƙasashen biyu suka bayyana a sanarwar haɗin gwiwa.

KU KUMA KARANTA: An bayar da shawarar kafa tarayyar ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso

“Ƙungiyar ta gaza cim ma nasara. Abin takaicin ma shi ne, babban burin ƙasashenmu na tabbatar da tsaro da ci-gaba a yankin G5 Sahel, ya fuskanci tarnaki daga gwamnatocin da suka gabata, abin da ya tabbatar mana cewa buƙatarsu ba ta dace da tsarinmu na samun ‘yanci da kamala, kamar yadda aka fayyace a shirin na G5 tun da farko,” in ji sanarwar.

A wani jirwaye mai kamar wanka da suka yi wa Faransa, ƙasashen biyu sun ƙara da cewa “bai zai yiwu ƙungiyar G5 Sahel ta rika cika muradin ƙasashen waje ba, alhali al’ummominmu suna shan wahala, kuma ana ba mu umarni kamar wasu ƙananan yara, a hana jama’armu ‘yanci.”

Leave a Reply