Ni na ƙara wa kaina maki a jarrabawar JAMB – Mmesoma

0
586

Daga Ibraheem El-Tafseer

Yarinyar nan da ake zargi da ƙara wa kanta maki a jarrabawar JAMB ta amince cewa ita da kanta ta sauya sakamakon jarrabawar.

Ejikeme Mmesoma mai shekarar 19, wadda tsohuwar ɗaliba ce a makarantar ‘Anglican Girls’ Secondary School’ a jihar Anambra, ta bayyana yadda ta ƙara wa kanta maki a takardar sakamakon jarrabawar.

A ‘yan kwanakin nan, batun ya janyo ce-ce-ku-ce, tun bayan da hukumar da ke shirya jarrabawar ta ƙaryata makin da ɗalibar ta yi iƙirarin samu a jarrabawar.

Ita dai hukumar JAMB ta ce ɗalibar ta samu maki 249, saɓanin maki 362 da take iƙirarin samu, to sai dai a lokacin ɗalibar ta kafe cewa sakamakon da take iƙirari shi ne na gaskiya.

KU KUMA KARANTA: JAMB zata duba yiwuwar amfani da wayoyin hanu a jarabawar UTME

Lamarin da ya sa gwamnan jihar Anambra Charles Soludo ya kafa wani kwamiti domin gudanar da bincike kan lamarin.

Kwamitin ya gayyaci ɗalibar da shugabar makarantar da kuma jami’an hukumar JAMB domin jin bahasin kowane ɓangare.

Hukumar ta JAMB ta ce sakamakon da ɗalibar ke iƙirarin samu wanda ke ɗauke da maki 362 sakamako ne na bogi, ba na gaskiya ba.

Haka kuma JAMB ɗin ta bayyana yadda Ejikeme Mmesoma ta yi ta yunƙurin neman samakamon jarrabawar tata a shafin hukumar cikin sa’o’i da dama, kuma a duk waɗannan lokuta sakamako ɗaya take samu daga hukumar wanda ke nuna cewa ta samau maki 249.

To sai dai Ejikeme Mmesoma ta shaida wa kwamitin cewa ta amince da wanna bayani da hukumar jami’an hukumar ta JAMB suka yi wa kwamitin.

Tana mai cewa da kanta ta ƙara makin sakamakon jarrabawar tata.

Ta ce ta yi amfani da wayarta wajen sauya sakamakon jarrabawar, kafin ta fitar da takardar sakamakon jarrabawar.

Kwamitin ya yi ƙoƙarin gano dalilin ɗalibar na aikata wannan laifi, to sai dai ta ce ba ta da wani ƙwaƙƙwararn dalili.

Daga ƙarshe kwamitin ya buƙaci ɗalibar ta gaggauta neman afuwa bisa wannan laifi da ta aikata, ta hanyar rubuta wasiƙar neman afuwa ga hukumar JAMB da hukumar Makarantar da ta kammala, sannan zuwa ga gwamnatin jihar Anambar.

Sannan kwamitin ya buƙaci ɗalibar ta je a duba lafiyar ƙwaƙwalwarta, tare da yin ƙira da duka ɗaliban da ke rubuta jarrabawar da su tsaya inda dokokin hukumar ya iyakance musu.

Leave a Reply