Ni na ba da shawarar a canza sunan Maryam Shetty a minista – Ganduje

0
195

Daga Ibraheem El-Tafseer

Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce wasu ‘yan ba-ni-na-iya ne suka bayar da sunan Maryam Shetty don naɗa ta minista daga Kano, ba tare da saninsa ba.

Sai dai, ya ce shugaban ƙasa yana da damar naɗa mutanen da yake son tafiya da su a muƙaman ministoci daga jihohin ƙasar bisa la’akari da tsare-tsarensa da ƙwarewar mutanen da kuma sauran buƙatu.

A wata hira da ya yi da wasu kafofin yaɗa labarai ciki har da Freedom Radio ranar Asabar, tsohon gwamnan, wanda shi ne jagoran jam’iyyar a Kano, ya ce ba shi da cikakkiyar masaniya a kan Maryam Shetty, hasali ma ba su santa ba a matsayinsu na jagororin APC daga Kano.

Don haka ”ka ga ba mu da wani ma’auni da za mu ce za ta iya, ko ba za ta iya wannan aiki ba idan aka nemi shawararmu”.

KU KUMA KARANTA: Dalilin da ya sa na janye sunan Maryam Shetty a matsayin minista – Tinubu

Ganduje ya ce martanin da mutane suka yi ta bayyanawa a shafukan sada zumunta, shi ma ya taka rawa wajen ɗaukar matakin sauya sunan Dakta Maryam Shetty, bayan wasu sun riƙa nuna cewa ba za ta iya riƙe muƙamin minista a Najeriya ba kasancewar ba ta taɓa riƙe wani muƙamin gwamnati ba.

Shugaban na APC ya ce da haka ne labari ya je har wajen shugaban ƙasa, wanda ya ƙira Ganduje don jin shawararsa.

”Ya ce min ga fa abin da ke faruwa, shin kai ka bayar da sunanta? Sai na ce masa a’a sam sam, ba ni ba ne, ban ma sani ba, daga nan ya ce to ya ka gani? akwai buƙatar a canza?, sai na ce masa ƙwarai da gaske kuwa”, in ji tsohon gwamnan na Kano.

Ganduje ya ce muƙamin minista, matsayi ne da ke buƙatar dattaku da sani (ƙwarewa), sannan yana buƙatar taka muhimmiyar rawa wajen kafa gwamnati a siyasance.

”To idan ka auna waɗannan abubuwa kuwa, ai mu ya kamata a tambaya, in dai ana so a bayar da wakilci daga jihar Kano”, in ji shi.

Ya ce ko da wani can ya bayar da wata shawara, to ya kamata a tuntuɓe su, idan ya dace sai su ba da goyon baya.

Cire sunan Maryam Shetty daga jerin ministocin Shugaba Tinubu, kamar bayyana sunanta a cikin waɗanda za a naɗa tun farko, ya yi matuƙar janyo muhawara musamman a tsakanin matasa da matan ƙasar.

Da yawa suna cewa abin da aka yi ya nuna rashin dacewa da kuma hangen nesa.

Leave a Reply