Ni ba ɗan yawan buɗe ido ba ne – Sanata Ndume

0
47
Ni ba ɗan yawan bude ido ba ne - Sanata Ndume

Ni ba ɗan yawan buɗe ido ba ne – Sanata Ndume

Sanata Ali Muhammad Ndume ya yi watsi da shugabancin da Majalisar Dattawa ta ba shi na kwamitin yawon buɗe ido.

Ndume ya yi wa nadin da aka bore ne yana mai cewa shi ba ɗan yawon buɗe ido ba ne.

Naɗin da kuma boren na Ndume na zuwa ne kwanaki biyu bayan Majalisar Dattawan ta tsige shi daga kujerarsa ta Babban Mai Tsawatarwa.

A ranar Laraba ne shugabancin Jam’iyyarsa a majalisar ya maye gurbinsa da Sanata Tahir Mungono (Borno ta Arewa).

Dambarwar Ndume a Majalisar na da nasaba da sukan da ya yi wa kamun ludayin Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wajen magance matsalar yunwa da tsadar rayuwa a Najeriya.

KU KUMA KARANTA: Barau Jibrin, Ndume da wasu sanatoci 38 na iya rasa kujerun su 

A wata wasika da Shugaban Jam’iyya APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya aika wa majalisar, ya buƙaci Ndume ya bar APC ya koma duk jam’iyyar adawar da ya zaɓa wa kansa.

Ganduje ya kuma buƙaci a sauƙe Ndume daga muƙaminsa na mai tsawatarwa, saboda abin da shugaban jam’iyyar ya ƙira kalaman da ba su dace ba da ke iya kawo wa shugaban ƙasar koma-baya.

Wannan lamari ya samo asali ne daga hirar da ɗan majalisar ya yi da manema labarai inda a ciki ya koka cewa shugaban ƙasa bai san ainihin halin da al’umma suke ciki ba.

A cewarsa, wasu sun kange shugaban ƙasar daga yin magana a kan lamurra da kuma ganin jama’a, ballantana a samu yadda za a fayyace masa halin da jama’a suke ciki.

Ɗan majalisar ya kuma koka da cewa ’yan Najeriya sun riga sun yi fushi saboda yunwa da lalacewar yanayin karfin aljihunsu, ba tare da gwamnatin da ɗauki kwarararan matakan magance matsalolin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here