Netanyahu ne ‘ba ya son kawo ƙarshen yaƙi a Gaza’ – Shugaban Hamas

0
176

Shugaban Reshen Siyasa na ƙungiyar Hamas, Ismail Haniyeh ya yi gargaɗi kan yiwuwar mamayar soji daga sojojin Isra’ila a Rafah, kuma ya ce haka zai iya haifar da kisan kiyashi kan Falasɗinawa.

A wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Anadolu ranar Asabar, Haniyeh ya ce, “Ina kira da duka ƙasashe ƙawayenmu, da ‘yan’uwanmu a Masar, da ‘yan’uwanmu a Turkiyya, da ‘yan’uwanmu a Qatar a matsayin masu shiga-tsakani, da ƙasashen Turai da su ɗauki matakin hana zaluncin (Isra’ila), don dakatar da hari kan Rafah, da kuma ficewar (sojin Isra’ila) gaba ɗaya daga Zirin Gaza da kawo ƙarshen hare-hare kan Gaza”.

KU KUMA KARANTA: Hamas da Islamic Jihad sun bayar da sharuɗa 4 na nasarar yarjejeniyar tsagaita wuta

Game da fafutukar Falasɗinawa, Haniyeh ya ce, “Idan maƙiyanmu ‘yan aƙidar Zionism suka shiga Rafah, al’ummar Falasɗinu ba za su zaɓi ajiye makami ba. Mayaƙanmu a Rafah sun shirya kare kansu da tirjiya ga azzalumai.”

Leave a Reply