NDLEA ta kama wani babban dilan ƙwaya a Kano

0
220
NDLEA ta kama wani babban dilan ƙwaya a Kano

NDLEA ta kama wani babban dilan ƙwaya a Kano

Daga Jameel Lawan Yakasai

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), reshen jihar Kano, ta ce ta kama wani fitinannen dilan miyagun kwayoyi, Faisal Yusuf Umar, mai shekaru 23, a Ƙaramar Hukumar Fagge.

KU KUMA KARANTA: NDLEA ta kama maniyyata a filin jirgin saman Kano, bisa zargin safarar hodar Iblis zuwa ƙasar Saudiyya

Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Sadiq Muhammad Maigatari ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano a yau Lahadi.

Ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan wani binciken sirri da aka gudanar sakamakon koken al’umma game da miyagun ayyukansa.

“A ranar 18 ga watan Yuli, jami’an NDLEA da ke ƙarƙashin rundunar, reshen Fagge sun gudanar da wani sintiri na musamman a gidan su wanda ake zargin da ke Dandali, a Ƙaramar Hukumar Fagge.

“An samu tarin kayan maye, ciki har da kwalabe 40 (kilo 4) na maganin tari na Benylin mai ɗauke da Codeine, tare da kuɗi har naira 204,000.00,” in ji shi.

Leave a Reply