Hukumar da ke yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya NDLEA ta kama wani gungun mutane da kilogiram 51.90 na tabar wiwi a wani samame da ta kai filin jiragen sama na Murtala Mohammed da ke jihar Legas.
Mutanen uku suna daga cikin wata ƙungiyar masu aikata manyan laifuka da suka ƙware a safarar miyagun ƙwayoyi a Najeriya da ƙasashen waje.
KU KUMA KARANTA: NDLEA ta kama wiwi da ake shirin kaiwa ƙasar Qatar
A wata sanarwa da NDLEA ta fitar ta ce ”An yi nasarar ƙwato jimillar kilogiram 51.90 na tabar wiwi daga gungun ƴan ƙungiyar da suka ƙware wajen safarar miyagun ƙwayoyi a Najeriya da Afirka ta Kudu da Mozambique da Turai da kuma Amurka”.
Sanarwar mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi ta bayyana cewa, NDLEA ta kwashe sama da watanni biyu tana neman gungun mutanen ruwa-a-jallo.
“An ƙwato miyagun ƙwayoyin da aka ɓoye su a cikin wasu kwalayen injinan yankan ƙarafa mai ƙarfin watt 2300 guda 15, tare da haramtattun ƙwayoyi da nauyinsu ya kai kilogiram 49.70 da aka ƙwato daga kayan aikin,” in ji sanarwar.
“Kazalika, an kama wani ƙarin kilogiram 2.2 a ma’ajiyar ƙungiyar da ke unguwar Ayobo a Legas,” in ji shi.
Hukumar ta bayyana cewa ta samu izinin wucin-gadi daga kotu don binciken gidaje da otal da motoci da kuma kuɗaɗen da ke da alaƙa da ƴan ƙungiyar bayan kamen.
Haka kuma, ”an ƙaddamar da farautar sauran ƴan kungiyar da suka gudu,” in ji sanarwar.
“An samu wannan nasara ce bayan kama biyu daga cikin gungun mutanen ranar Juma’a, 19 ga Afrilu, Onyinyechi Irene da Frankline Uzochukwu a jihar Legas da Awka, Anambra.
“Haka kuma an kama Osita Obinna wanda shi ma yana daga cikin waɗanda muke nema ruwa-a-jallo a Legas,” a cewar sanarwar.