Hukumar da ke yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta kama wani gawurtaccen mai safarar miyagun ƙwayoyi wanda ya taɓa tserewa daga gidan yarin Kuje.
Hukumar ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi inda ta ce jami’anta sun kama Ibrahim Momoh wanda aka fi sani da Ibrahim Bendel a maboyarsa da ke Filin Dabo da ke unguwar Dei-Dei a Abuja.
An kama Ibrahim Momoh a karon farko a ranar 27 ga watan Nuwambar 2014 da tabar wiwi mai nauyin kilo 385.1 inda kotu ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara bakwai da rabi a ranar 22 ga watan Yulin 2015.
Sai dai Momoh ɗin ya tsere daga gidan yarin na Kuje a ranar 16 ga watan Mayun 2016, kamar yadda hukumar ta NDLEA ta bayyana.
“Bayan samun bayanan sirri, NDLEA a ranar 20 ga watan Nuwambar 2022 ta kai samame ɗakin ajiye kayayyaki na Ibrahim Momoh wanda ya tsere daga gidan yari, inda aka gano manyan buhuna 81 na wiwi masu nauyin 1,278.
KU KUMA KARANTA: Hukumar NDLEA a Imo ta tabbatar da kashe jami’anta biyu tare da wasu jami’an tsaro uku
“Ɗakin ajiye kayayyakin na a gonar kajinsa da ke Dei-Dei da ke Abuja,” in ji sanarwar.
Hukumar ta ce Momoh ba ya gonar a lokacin da suka kai samame gonar sai dai manajan gonar mai suna Richard Forson dan kasar Ghana wanda aka kama sannan aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara biyu.
“An samu nasara a neman da ake yi wa gawurtaccen mai safarar ƙwayoyin a ranar 5 ga watan Nuwambar 2023 a lokacin da jami’an NDLEA suka sake kai samame a gonarsa da ke Filin Dabo inda aka kama shi da kilo 56.9 na wiwi da kuma gram 42.7 Na Diazepam,” in ji NDLEA.