NDLEA ta kama dillali da ke sayarwa ‘yan bindiga ƙwayoyi a Zamfara da Kebbi

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) ta kama Agu Amobi, wani ɗan kasuwa mazaunin Qatar, a filin jirgin sama na Murtala Muhammed, da ke Lagos, bisa zargin safarar ƙwayoyi.

Cewar sanarwar da ya fitar ranar Lahadi, Femi Babafemi, mai magana da yawun NDLEA, ya ce an kama wanda ake zargin ranar Asabar yayin da ya ke ƙoƙarin ƙetarewa zuwa Doha ta jirgin Qatar Airways, Legit Hausa ya wallafa.

Ya ce an kama Amobi da kilo 1.30 na tabar wiwi da aka nade a jakar kayan abinci.

Babafemi ya ce wanda ake zargin ya yi ikirarin a Qatar ya ke zaune sama da shekara 10 kuma ya na siyan ƙwayoyi daga Enugu ya kai Doha don ya samu ya biya kuɗin makarantar yaransa uku.

KU KUMA KARANTA: NDLEA ta kama ƙwayoyin Tramadol sama da miliyan bakwai da kwalaben Kodin kusan 100,000

A wani makamancin rahoton a rana guda, Uchegbu Obi ya shiga hannu bayan an kama shi da ƙwayar tiramol da ta kai 72,000 a MMIA.

An ruwaito cewa Obi yayi ƙoƙarin aika ƙwayar daga Lagos zuwa Kano.

Hukumar ta kuma tabbatar da kama mutum uku Musa Sani, Mohammed Ibrahim da kuma Adamu Usman da kurkura ɗauke da wiwi da nauyinta ya kai 15 da kuma kwarya har guda 128,500 a Jihar Yobe.

Hukumar ta kuma wani mai shekaru 45 Yusuf Yahaya a jajeberin Kirismeti a hanyar Lagos zuwa Ibadan da kilo 31 na tabar wiwi a wata motar haya da ta taso daga Ibadan, jihar Oyo, zuwa Jihar Kebbi.

Babafemi ya ce daga binciken da suka gudanar an gano Yahaya ya na safarar miyagun ƙwayoyi ne ga yan bindiga a yankunan Kebbi da Zamfara

Babafemi ya ce daga binciken da suka gudanar an gano Yahaya ya na safarar miyagun ƙwayoyi ne ga yan bindiga a yankunan Kebbi da Zamfara.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *