NDLEA ta kama dattijo mai shekaru 75, da Tabar Wiwi
Daga Jameel Lawan Yakasai
Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta kasa NDLEA ta cafke mutane da dama a jihohi daban-daban tare da kwace tarin miyagun ƙwayoyi a cikin makon da ya gabata.
A Taraba, jami’an NDLEA tare da sojoji da sauran jami’an tsaro sun ƙona tan 178,750 na wiwi daga gona mai faɗin hekta 71.5, inda suka kama wani matashi mai shekara 30 da bindiga.
A Anambra kuwa, wani tsoho mai shekara 75, Uchelue Ikechukwu, ya shiga hannu da kilo 26.7 na wiwi, tare da wasu mutum shida.
KU KUMA KARANTA: NDLEA a Kano ta cafke matashi da tabar wiwi ta sama da Naira Miliyan 10
Haka kuma, a Kaduna, an kama 104,900 tramadol da aka ɓoye cikin tankar mai da ake zargin za a kai ga ’yan ta’adda a Borno, inda aka kuma cafke babban dillali a Maiduguri da dubban kwayoyi da kuma kuɗi sama da N7.9m.
A Kano, Adamawa, Nasarawa, Edo, Ondo, Lagos da Ekiti ma, an kama dubban tramadol, exol-5, codeine, Loud, Colorado da methamphetamine daga hannun dillalai da matasa.
Shugaban hukumar NDLEA, Brig. Gen. Buba Marwa (Rtd), ya yaba da jami’an hukumar bisa wannan aiki tare da ci gaba da wayar da kai ga jama’a kan illar miyagun ƙwayoyi.









