No menu items!

Sample Page Title

Date:

Hukumar da ke yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce ta yi kamen miyagun ƙwayoyi masu dumbin yawa daf da Bikin Kirisimeti.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa daga cikin miyagun ƙwayoyin da ta kama har da ƙwayoyin Tramadol sama da miliyan bakwai da kwalaben maganin tari mai dauke da kodin kusan 100,000.

Hukumar ta ce ta kama kwayoyin na Tramadol a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas tare da da haɗin gwiwa da jami’an kwastam da sauran jami’an tsaro.

Hukumar ta ce an shigo da ƙwayoyin ne daga birnin Hamburg na Jamus. A cewar sanarwar, kwayoyin na cikin manyan kwalaye 100 waɗanda baki ɗayansu nauyinsu ya kai kilo 7,150.

KU KUMA KARANTA: NDLEA ta kama gawurtaccen mai safarar wiwi shekara bakwai bayan ya tsere daga gidan yari

Haka kuma hukumar ta ce jami’anta da ke aiki a Legas sun kai wani samamen a wasu shaguna biyu a ranar Laraba 20 ga watan Disamba a kasuwar duniya da ke yankin Ojo.

NDLEA ta ce bayan sun yi bincike sai suka gano kwali 258 na maganin tari na ruwa mai ɗauke da kodin da kuma kwali takwas na kodin din amma na ƙwaya.

Kwalayen na ɗauke da kwalabe 49,200 na maganin tarin na ruwa sai kuma kwayoyi 46,200.

Hukumar ta ce washe gari jami’an hukumar sun kai samame a wani gida a unguwar Mushin ta ke jihar ta Legas inda suka kama wata dattijuwa mai shekara 70 mai suna Selifat Funke Cole da ɗanta Babajide Ayorinde Cole inda aka kama su da kilo 117.900 na wiwi.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...