NDLEA ta bankaɗo ɗakin da ake haɗa sinadaran ƙwayar meth, ta ƙwato fakitin haramtattun ƙwayoyi da dama

1
625

Jami’an hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) sun gano wani ɗakin bincike na sirri da ke samar da sinadarin ‘Methamphetamine’ a Ikeja da ke Legas.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Femi Babafemi ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Mista Babafemi ya ce an gano buhunan maganin da wasu sinadarai na farko da aka yi amfani da su wajen samar da su.

KU KUMA KARANTA: Hukumar NDLEA ta ƙwato miyagun ƙwayoyi mai nauyin 390 a jihohi 4 cikin kwanaki 5

Ya ce jami’an da ke yaƙi da muggan ƙwayoyi sun kai samame a ɗakin gwaje-gwaje na ɓoye da ke lamba 4, Titin Bode Oluwo, Mende, Maryland a Ikeja a ranar 6 ga watan Yuni.

Wannan ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da sa ido sun tabbatar da samar da muggan ƙwayoyi a ginin. In ji shi.

“A ƙarshen binciken, an riga an samar da kilogram ɗaya na ƙwayar ‘methamphetamine’ dake ƙunshe, an gano adadin sinadarai na farko.

“An ƙwato sauran kayayyakin da aka yi amfani da su wajen samar da muggan ƙwayoyi daga gidan yayin da ake ƙoƙarin cafke mai gidan da ya gudu,” inji shi.

Mista Babafemi ya kuma ce jami’an hukumar a ranar 5 ga watan Yuni, sun kama wasu mutane biyu, Wasiu Saliu da Afolabi Banjo ɗauke da hodar ‘skunk’ kilo 247 a unguwar Oyingbo da ke Legas.

Ya ce an kama wani wanda ake zargi, Tijjani Damilola a Isheri da lita 12.5 na ‘skuchies’ da tabar wiwi mai nauyin kilogram 98 na wani wanda ake zargi da ya gudu.

Daraktan ya ƙara da cewa an ƙwato kilogram 12.5 na abu ɗaya daga hannun wani Adebowale Babatunde bayan an kama shi a Mushin a ranar 8 ga watan Yuni.

1 COMMENT

Leave a Reply