No menu items!

Sample Page Title

Date:

NCC ta umarci kamfanonin sadarwa da su sake buɗe layukan mutane da suka rufe

Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), ta umarci kamfanonin sadarwa da su sake buɗe layukan wayar mutane da suka rufe.

NCC, ta ce mutane ba su samu isasshen lokaci wajen haɗa lambar shaidar ɗan ƙasarsu ta (NIN) da layukan wayoyinsu ba.

Hukumar ta ce sake buɗe layuka ba zai ɗauki lokaci ba, amma zai bai wa mutane damar sake haɗa layukansu da lambar NIN ɗinsu.

Mutane da dama sun gaza amfani da layukansu sakamakon kulle su da kamfanonin sadarwa irin su MTN, Airtel, Glo da 9Mobile suka yi a ƙarshen mako.

Sai dai rufe layukan na cikin manufar gwamnati na buƙatar duk masu amfani da waya dole su haɗa NIN ɗinsu da layukansu.

KU KUMA KARANTA: Kamfanonin sadarwar na ƙoƙarin dawo da ayyukansu, bayan katsewar intanet – NCC

An fara haɗa lambar NIN da layin waya a watan Disamban 2020.

An ɗage wa’adin rufe haɗa lambar da layukan waya zuwa ranar 31 ga watan Yuli, 2024, domin bai wa mutane damar yin rajistar.

Duk da wannan tsawaita lokaci, mutane da dama ba su haɗa lambar NIN da layukan wayoyinsu ba.

Manufar gwamnati ita ce inganta tsaron ƙasa da tabbatar da samun bayanan ’yan ƙasa da ke amfani da layukan waya.

Haɗa lambar NIN da layukan wayoyi na taimakawa wajen tabbatar da ainihin bayanan mutane.

NCC ta ƙira ga waɗanda ba su kammala haɗa layukansu da lambar NIN ba da su gaggauta yi domin gujewa sake toshe layukansu.

Rahotanni da ke fitowa daga wasu yankuna, sun nuna yadda aka yi wa ofishin kamfanin sadarwa na MTN cikar ƙwari a safiyar ranar Litinin.

Lamarin ya kai wasu ga bai wa hammata iska, kan ganin an sake buɗe musu layukan da aka rufe.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...