NCC ta ƙwace jabun litattafai na kimanin Naira miliyan 5.7 a Enugu

0
75
NCC ta ƙwace jabun litattafai na kimanin Naira miliyan 5.7 a Enugu

NCC ta ƙwace jabun litattafai na kimanin Naira miliyan 5.7 a Enugu

Hukumar Kare Haƙƙin Wallafa ta Ƙasa, (NCC), ta kama wasu litattafai da aka kwaikwayon wallafa na sama da Naira miliyan 5.7 a wasu makarantu Enugu.

Da ta ke jawabi yayin aikin ƙwace littattafan , Darakta a NCC, ofishin Enugu, Ngozi Okeke, ta ce aikin na daga cikin yunƙurin hukumar na kawo ƙarshen satar wallafa a Enugu.

Ta jero sunayen littafan da ta ƙwace har da Ugo.C. Ugo- English and Mathematics series, New School Physics and Chemistry for Secondary Schools by Africana First Publishing Company da dai sauransu.

KU KUMA KARANTA:NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Okeke ta ce an kwace litattafan daga kamfanonin buga littattafai daban-daban, wadanda aka jibge a cikin shagunan sayar da litattafai na makarantu da ke shirin sayar wa daliban.

“Mun yi amfani da lokacin dawowa hutu, lokacin da masu satar wallafar ke sheke ayar su, mu kuma mu ke sa ido da binciken kwakwaf da kuma gudanar da ayyukan yaki da satar wallafa a wasu makarantun da ke sayen litattafai a wajen su.

“Darajar litattafan da aka kwace sun kai Naira miliyan 5.7,” in ji ta.

Okeke ta kuma bukaci jama’a da su marawa hukumar baya da sahihan bayanai da za su iya ba su damar magance matsalar satar wallafa a jihar.

Leave a Reply