Barista Abubakar Madaki, shi ne babban Darakta na Hukumar Kula da zubar da Shara a Jihar Nasarawa (NASWAMA) ya gargaɗi jama’a da su guji zubar da shara a magudanan ruwa da sauran wuraren taruwar jama’a, musamman a lokacin damina domin hana ɓarkewar annoba da ambaliya.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Malam Yusuf Gurku, jami’in yaɗa labarai na NASWAMA kuma ya miƙa wa manema labarai ranar Lahadi a ƙaramar hukumar Karu ta jihar.
A cewar Gurku, Madaki ya yi wannan gargaɗin ne saboda ya zama dole idan aka yi la’akari da illolin da ƙishi ke haifarwa ga lafiyar ɗan Adam da tabbatar da tsaftar muhalli da kuma rayuwar al’ummar jihar baki ɗaya.
KU KUMA KARANTA: Zan ƙwace wuraren zubar da shara da aka mayar da su wuraren kasuwanci – Gwamnan Sakkwato
“Hukumar kula da sharar gida tana yin iya ƙoƙarinta wajen tsaftace muhalli amma kuma haƙƙi ne da ya rataya a wuyan kowa da kowa ya ƙarawa ƙoƙarin gwamnati ta hanyar tsaftace muhallinsu.
“Ina so in yi amfani da wannan kafar domin yin ƙira ga ‘yan jiharmu masu bin doka da oda da su guji zubar da shara a magudanan ruwa da wuraren da ba a keɓe ba, la’akari da illar da ke tattare da lafiyar bil’adama.
Gurku ya naƙalto Madaki ya ce “Zubar da shara a magudanan ruwa, manyan tituna da wuraren taruwar jama’a na da haɗari ga lafiyar ɗan Adam kuma yana iya haifar da yaduwar cututtuka.”
Daga nan sai ya ƙara da cewa NASWAMA tuni ta ƙara ƙaimi wajen daƙile zubar da shara ba bisa ƙa’ida ba, inda ya ƙara da cewa duk wanda aka samu da aikata laifin zai fuskanci fushin doka.
Ya kuma yi ƙira ga masu bin doka da oda da su kai rahoto ga duk wanda aka kama da laifin zubar da abin ƙi ba bisa ƙa’ida ba ga hukuma ko jami’an tsaro a jihar domin a ɗauki matakin da ya dace a kansu saboda rashin bin doka.