Nan da 2027, za a na samun wutar lantarki na tsawon awa 20 a kullum a Najeriya

0
90
Nan da 2027, za a na samun wutar lantarki na tsawon awa 20 a kullum a Najeriya

Nan da 2027, za a na samun wutar lantarki na tsawon awa 20 a kullum a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta bayyana niyyar ta fara samar da wutar lantarki na tsawon sa’o’i 20 a kullum, zuwa nan da shekara 2027.

Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara akan harkokin Makamashi, Madam Olu Verheijen ce ta yi wannan bayani a birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu, inda ta kasance cikin mutanen da suka wakilci Najeriya a wurin taron da ya hada kan kasashen nahiyar a wurin bukukuwan Makon Makamashi na Afirka dake gudana a birnin na Cape Town.

To sai dai, furucin da Madam Verheijen ta yi, ya dau hankalin Alhaji Idris Mohammed, kwararre a fanin Makamashi kuma wanda ya taba rike shugabancin Kamfanin bada Wutar Lantarki na jihar Kaduna wanda ya bayyana cewa tun zamanin Mulkin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ne ake yi wa yan kasuwa tayin su zo su zuba jari a bangaren makamashi amma kuma har yau wannan kira bai karbu ba.

KU KUMA KARANTA:‘Yan Najeriya na kuka da taɓarɓarewar wutar lantarki a ƙasar

Idris ya ce an jima ana samun kalubale a bangaren Makamashi a kasar, shi yasa Madam Olu ta yi wannan kira ga ‘yan kasuwa su zo su zuba hannun jari a bangaren makamashi.

Shi ma mai pashin baki akan al’amuran yau da Kullum Abubakar Aliyu Umar, ya tofa albarkacin bakin sa, inda ya bayyana cewa “wannan yaudara ce kawai domin ya zuwa yanzu, ana ta kashe makudan kudade kan harkar makamashi a Najeriya amma har yanzu bai haifar da da mai ido ba. Abubakar ya ce Shugabanin suna yin abinda suka gadama ne kawai a duk lokacin da suka samu dama, sannan ya bayyana wadannan kalaman da aka bayyana da abin kunya.

Amma ga Mallam Aminu Jumare, wani dan kasuwa mazaunin birnin Abuja wanda yake amfani da wutar lantarki a kasuwancin sa, ya bayyana ra’ayin da ya saba da bayyanan da suka gabata, inda ya nuna cewa lallai aiki babba a gaba amma idan Gwamnati za ta iya fitar da makudan kudade don farfado da harkar makamashi, lallai za ta iya cika wannan buri na sa’o’i 20 a duk wuni zuwa shekarar 2027. Jumare ya ce sai dai kuma akwai tulin basussukan da Gwamnati ta ciyo, wadanda suke neman su fi karfin ta.

Leave a Reply