‘Nan ba da jimawa ba za’a shawo kan matsalar tsaro, farashin kayan abinci zai sauƙa’ – Kakakin Majalisa

0
112

Daga Ibraheem El-Tafseer

Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Tajudeen Abbas ya ce majalisar na sane da halin matsalar tsaro da tsadar rayuwa da ‘yan ƙasar ke fuskanta.

Honarabul Tajudeen Abbas ya ce a ɓangarensu na majalisa ba za su zuba wa ɓangaren zartaswa ido ba har sai an samu mafita.

Kakakin majalisar ya tabbatar wa da BBC cewa za a shawo kan ƙalubalen da ake fuskanta nan ba daɗewa ba.

”Majalisa za ta yi duk abin da ya kamata domin ganin an samu sauƙi a matsalar tsaro da tsadar rayuwa da ke fuskanta a ƙasar nan”.

KU KUMA KARANTA: Najeriya ta nemi taimakon Faransa kan matsalar tsaro

Kakakin majalisar ya ce majalisa ta za ƙirawo duka masu ruwa da tsaki a harkar tsaro domin magance matsalar tsaron da ake ciki.

Honarabul Tajedeen Abbas ya ce ‘yan majalisar na sane da irin halin matsin rayuwa da talakawan ƙasar ke ciki, kuma suna duk mai yiwuwa domin magance matsalar.

Don haka ne ma ya ce ‘yan majalisar suka mayar da hankali wajen sayen kayan abinci domin rabar wa talakwan da suka zaɓe su.

Ya kuma ce gwamnati na yin duk mai yiwuwa don magance matsalar, kuma ya tababtar da cewa nan ba da jimawa ba farashin kayan abincin zai sauka a ƙasar.

Leave a Reply