Najeriya za ta samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt dubu 14 – Ministan Lantarki
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa tana yunƙurin samar da wutar lantarki mai ƙarfin Megawatt 14,000 ta hanyar amfani da madatsun ruwa, lamarin da masana ke cewa gwamnatocin baya sun sha ɗaukar irin wannan alƙawarin, amma a ƙarshe kuɗaɗen da ake warewa ke salwanta.
Ministan wutar lantarkin Najeriya Adebayo Adelabu, ya ce Najeriya na da isassun madatsun ruwa da za su iya samar da hasken wutar lantarki mai karfin Megawatt 14,000.
Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da suka cimma yarjejeniya da Ministan ma’aikatar ruwa Joseph Utsev, da nufin cimma muradun Bankin Duniya na samar da isasshen hasken wutar lantarki da kuma bunƙasa harkar noma a Najeriya.
Ministan ya kara da cewa yanzu madatsun ruwan kasar na samar da kaso 20 cikin 100 na wutar lantarki mai karfin Megawatt 5,000, hakan ya sa suke yunƙurin faɗaɗa shi.
A hirarsa da Muryar Amurka, Injiniya Dakta Aminu Sahabi, wanda masani ne a harkar na’urorin samar da hasken wutar lantarki, ya ce Najeriya za ta iya samar da fiye da adadin Megawatt 14,000, domin tana da albarkatun samar da hasken wutar lantarki a kasar.
Ya kara da cewa, a yanzu haka Najeriya na buƙatar Megawatt sama da 45,000 kafin ta wadatar da ‘yan kasar da wutar lantarki.
KU KUMA KARANTA:Nan da 2027, za a na samun wutar lantarki na tsawon awa 20 a kullum a Najeriya
Injiniyan ya kuma ce, sai kasar ta yi amfani da sauran hanyoyin samar da wutar lantarki domin ta iya cimma wannan manufa.
Komred Isa Tijjani, na daga cikin masu sharhi kan lamurran yau da kullum, ya bayyana cewa wannan yunkuri na samar da wutar lantarki kawai tarihi ne zai maimaita kansa.
Tijjani ya kara da cewa a lokacin Shugaba Olusegun Obasanjo, an ware makudan kudade domin inganta harkar wutar lantarki a kasar, amma a karshe duk da kuɗaɗen da aka kashe haƙa ba ta cimma ruwa ba, kuma ba’a san inda kudaden suka sulale ba.
Yanzu kasar dai na samar da ƙasa da Megawatt 5,000 na lantarki ga mutane sama da miliyan 200, kuma a shekarar nan an fuskanci daukewar wutar lantarki sau 11 a kasar.