Najeriya za ta karɓi alluran rigakafin ƙyandar biri dubu 11, 200 – GAVI

0
7
Najeriya za ta karɓi alluran rigakafin ƙyandar biri dubu 11, 200 - GAVI

Najeriya za ta karɓi alluran rigakafin ƙyandar biri dubu 11, 200 – GAVI

Wannan wani ɓangare ne na rukunin farko na alluran rigakafi 899, 000 da aka bayar ta hannun ƙawancen AAM ga ƙasashen Afirka 9 inda annobar tafi ƙamari.

A yau Juma’a Najeriya za ta karbi rukunin farko na alluran rikafin kyandar biri, 11, 200, da gwamnatin Amurka ta bada gudunmawa da taimakon kawancen “GAVI”, dake fafutuka a kan alluran rigakafi.

KU KUMA KARANTA:UNICEF, WHO, CDC sun yi haɗin gwiwar samar da rigakafin ƙyandar biri

Sanarwar da shugaban kawancen GAVI, Dr. Sania Nishtar, ya fitar a yau tace anyi safarar alluran rigakafin zuwa Abuja, sakamakon yarjejeniyar da GAVI ya kulla ta taimakawa wajen samo gudunmawar alluran rigakafin kyandar biri 305, 000 domin agazawa kokarin duniya da nahiyar Afirka na yaki da cutar.

A ranar 24 ga watan Satumban da ya gabata, Amurka ta sanarda aniyarta ta bada gudunmawar alluran rigakafin kyandar biri da yawansu ya kai miliyan 1 domin tallafawa yaki da annobar tare da fara tattaunawa da GAVI a kan bada gudunmawar rukunin farko na allurai 305, 000.

Wannan wani bangare ne na rukunin farko na alluran rigakafi 899, 000 da aka bayar ta hannun kawancen AAM ga kasashen Afirka 9 inda annobar tafi kamari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here