Najeriya za ta fara ƙera wa sojoji wadatattun kayan aiki – Bello Matawalle

0
32
Najeriya za ta fara ƙera wa sojoji wadatattun kayan aiki - Bello Matawalle

Najeriya za ta fara ƙera wa sojoji wadatattun kayan aiki – Bello Matawalle

Daga Ali Sanni Larabawa

Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba Najeriya zata riƙa ƙera wa kanta wadatattun kayayyakin aikin da sojojin ƙasar ke buƙata.

Ya bayyana hakan ne lokacin da yake wa manema labarai jawabi yayin da ya halarci taron murnar cika shekaru 60 da kafa Kamfanin Ƙera Kayan yaƙin sojoji wato, DICON, wanda a shekarun baya aka fi sani da DIC.

Ministan ya ƙara da cewa Kamfanin DICON ya taka muhimmiyar rawa wajen ƙera kayan tsaron ƙasar ta hanyar haɗin guiwa da kuma ƙirƙirar abubuwa da dama.

KU KUMA KARANTA: Ba za mu bar kangararru su rusa mana ƙasa ba – Rundunar Tsaron Najeriya

Ya ce saboda haka DICON zai ci gaba da taka rawa wajen bayar da gudummawar sa don tabbatar da tsaro mai inganci da bunƙasa tattalin arziki.

A taron yace masu mulki da kuma masu ruwa da tsaki su haɗa kai domin cimma nasara.

“Za’a gudanar da taron ADIC a ranakun Laraba da Alhamis a cibiyar taro ta Shehu Musa ‘Yar’Adua, Abuja.

“Za a tattauna batutuwa da suka jiɓanci fasahar kayan tsaron ƙasa na sojoji a Afrika.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here