Najeriya ta zama ƙasa ta biyu wadda ta fi yawan talakawa a duniya — Tsohon shugaban NBS

0
165
Najeriya ta zama ƙasa ta biyu wadda ta fi yawan talakawa a duniya — Tsohon shugaban NBS
Tsohon shugaban NBS

Najeriya ta zama ƙasa ta biyu wadda ta fi yawan talakawa a duniya — Tsohon shugaban NBS

Tsohon shugaban Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), Yemi Kale, ya bayyana cewa sama da mutane miliyan 89, wato kashi 40% na al’ummar Najeriya, suna rayuwa ƙasa da layin talauci.

Ya bayyana haka ne a taron The Platform Nigeria na ranar ‘yancin kai, inda ya ce Najeriya ta zama ƙasa ta biyu a duniya da ta fi yawan talakawa, bayan Indiya.

Kale ya danganta hakan da kuskuren manufofi da jinkirin aiwatar da gyare-gyare da ya kamata a soma tun sama da shekaru goma da suka gabata.

KU KUMA KARANTA: NBS ta ayyana Yobe a matsayin jihar da ta fi kowace jiha sauƙin rayuwa

Ya ce hakan ya jefa al’umma cikin tsananin matsin tattalin arziki da hauhawar farashin kaya.

Ya bayyana cewa sabbin gyare-gyaren tattalin arziki da ake aiwatarwa yanzu na da zafi, amma babu wata madaidaiciyar mafita a madadinsu.

Ya ce idan aka gudanar da su da gaskiya da daidaito, za su iya juya damar Najeriya zuwa ci gaba mai amfani ga kowa.

Kale ya bukaci gwamnati ta tabbatar da dorewar manufofin tare da ƙarfafa tsare-tsaren kariya ga jama’a, domin tafiyar gyare-gyaren ta kasance mai adalci da amfanar al’umma baki ɗaya.

Leave a Reply