Najeriya ta tabbatar mutum 85 sojoji suka kashe bisa kuskure a Kaduna

0
137

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Najeriya ta tabbatar da cewa aƙalla farar hula 85 sojojin ƙasar suka kashe a wani hari bisa “kuskure” da sojojin suka ce sun kai a ƙasar a ranar Lahadi.

Rahotannin da aka samu daga farko sun ce mutum 30 aka tabbatar sun rasu a ƙauyen Tudun Biri a Jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin.

“Ofishin Arewa Maso Yammaci ya samu bayanai daga ƙaramar hukuma kan cewa an binne gawarwaki 85 a daidai lokacin da ake ci gaba da bincike”, kamar yadda NEMA ta bayyana a wata sanarwa a ranar Talata.

Hukumar ta ce aƙalla mutum 66 suke karbar magani a asibitoci da ke Kaduna.

KU KUMA KARANTA: Zulum yana jefa rayuwarsa cikin hatsari don ƙarfafa gwiwar sojojin Najeriya — Badaru

Tuni shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan yadda lamarin ya faru inda ya ce “abin takaici ne”.

A ranar Litinin, Kwamishinan wucin-gadi na Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan yadda aka kashe waɗannan farar hula.

Kwamandan runduna ta ɗaya da ke Kaduna VU Okoro ya tabbatar da cewa sojojin na gudanar da ayyuka ne a kan ‘yan ta’adda amma bisa kuskure suka kai hari kan farar hula.

Leave a Reply