Najeriya ta naɗa Finidi George sabon kocin Super Eagles

0
95

A jiya Litinin ne kwamitin gudanarwa na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya, NFF, ya karɓi shawarar kwamitin ƙwararru na hukumar, don naɗa Finidi George mai shekara 52, a matsayin sabon babban kocin tawagar maza ta ƙasar, Super Eagles.

Finidi George tsohon ɗan wasan Super Eagles ne da ke buga wasa a gaba. Ya kwashe watanni 20 a matsayin mataimakin tsohon koci Jose Peseiro, kafin ɗan Portugal ɗin ya ajiye aiki bayan kammala gasar kofin Afrika ta AFCON.

Bayan tafiyar Peseiro, Finidi ne ya ci gaba da riƙe ƙungiyar a matsayin babban koci na riƙo, inda ya jagoranci tawagar a wasanni biyu na sada-zumunta da ta buga a Maroko a watan jiya.

A wasannin biyu, Finidi ya jagoranci Super Eagles suka yi nasara kan tawagar Black Stars ta Ghana da ci 2-1. Sai dai a wasansu da Mali, sun yi rashin nasara da ci 0-2.

KU KUMA KARANTA: Ba za a manta da Pele ba, in ji hukumar kwallon kafa ta FIFA

Finidi George yana cikin shahararriyar tawagar Najeriya da ta ci kofin ƙasashen Afirka na shekarar 1994, wadda aka buga a Tunisia, sannan suka yi bajinta a karon farko da Najeriya ta je gasar cin kofin duniya da aka yi a wannan shekarar a Amurka.

Ɗan wasan ya buga wa Najeriya wasa har sau 62 inda ya je gasanni biyu na kofin duniya a 1994 da 1998. Sannan ya ciyo lambar yabo a gasannin kofin Afrika da aka buga a shekarun 1992, da 1994, da 2000, da 2002.

Lokacin yana ganiyarsa, Finidi ya buga wa manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Turai kamar Ajax Amsterdam, ta Netherlands, da Real Betis ta Sifaniya. A gida Najeriya kuwa, ya buga wa Calabar Rovers da Sharks FC.

Babban aikin da ke gaban sabon kocin shi ne horar da Super Eagles ta shirya wa wasan neman gurbi a gasar kofin duniya ta 2026, inda Najeriya za ta kara da Afirka ta Kudu, da kuma Benin a birnin Uyo da kuma Abidjan, nan da makonni biyar.

Leave a Reply