Connect with us

Ƙasashen Waje

Najeriya ta maida wa Nijar wutar lantarki

Published

on

Najeriya ta amince ta maido da wutar lantarki da ta yanke wa Jamhuriyar Nijar bayan ƙungiyar ECOWAS ta dage takunkumin da ta kakaɓawa ƙasashen Nijar din da Mali da Burkina Faso kuma Guinea.

ECOWAS ta dage takunkumin ne bayan babban taron kungiyar kan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro da ya gudana a fadar gwamnatin Najeriya da ke Abuja.

Shugaban Najeriya kuma shugaban ECOWAS, Bola Tinubu, ya ce, saboda haka “Najeriya sa ta dawo da wutar lantarki da ta yanke wa Nijar ba tare da bata lokaci ba.”

A watan Agustan bara ne Najeriya ta katse wutar lantarki da take ba wa Nijar a matsayin wani bangare na takunkumin da ECOWAS ta kakaɓa saboda juyin mulkin da sojojin Nijar suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum.

Al’ummar Nijar, musamman mazauna manyan birane sun shiga damuwa saboda rashin wutar lantarkin.

A watan Nuwamba ne dai sanatoci daga Arewacin Najeriya suka bukaci Tinubu ya mayar wa Nijar wutar.

A ranar Asabar kuma shugaban da kansa ya yi kira da ECOWAS ta dage jingine tattalin arzikin da ta kakaɓawa kasashen Nijar, Mali, Burkina Faso da Guinea.

KU KUMA KARANTA: Al’ummar Nijar na maraba da matakin ECOWAS na janye musu takunkumi

A cewarsa, an sanya takunkumin ne da nufin shawo kan shugabannin gwamnatocin sojin ƙasashen zuwa teburin tattaunawa.

Ya bayyana cewa ƙungiyar ta ɗauki matakinta ne bisa kyawawan manufofin yankin na tsaro, zaman lafiyar al’umma, mulkin dimokuraɗiyya, ’yancin siyasa, yalwar arziki da ci gaban tattalin arziki mai dorewa ta hanyar samar da dama ga kowa a yammacin Afirka.

Ya ce babu wata ƙiyayya ko boyayyar manufa a cikin matakan da aka dauka kuma babu wata manufa ta ruguza halastacciyar manufar siyasa ta kowace kasa ko cigaban wani ɓangare.

Da haka ne Tinubu ya buƙaci ƙungiyar da ta saukaka shigar da kayayyakin abinci da magunguna da sauran kayayyakin jin kai ba tare da katsewa ba ga al’ummar waɗannan ƙasashe, musamman ma waɗanda suka fi kowa rauni.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ƙasashen Waje

Dakta Mas’ud Pezeshkian ne lashe zaɓen shugaban ƙasar Iran

Published

on

Dakta Mas'ud Pezeshkian ne lashe zaɓen shugaban ƙasar Iran

Dakta Mas’ud Pezeshkian ne lashe zaɓen shugaban ƙasar Iran

Daga Ibraheem El-Tafseer

Waye Dakta Mas’ud Pezeshkian sabon shugaban ƙasar Iran na 9 cikin shekaru 45 ataƙaice?

An haife shi a ranar 29 ga Satumba, 1954, a Mahabad, a yammacin lardin Azarbaijan, Dakta Mas’ud Pezeshkian ya wakilci birnin Tabriz da ke arewa maso yammacin kasar a majalisar dokokin Iran ta 12.

Ya riƙe muhimmin muƙamai a majalisar a Hukumomi daban-daban matakin gwamnatin tarayya, kuma ya zama ministan lafiya a lokacin mulkin Shugaba Mohammad Khatami (2001-2005). Duk da cewa an tsige shi bayan wasu lokuta saboda gaza cimma wasu ayyuka da kawo sauyi.

An zaɓe Pezeshkian a majalissar 8th, 9th, 10th, and 11th. A tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020, ya kuma rike mukamin mataimakin shugaban majalisar na farko. A baya dai ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2013 da 2021 amma ya kasa samun nasara a lokuta biyun.

KU KUMA KARANTA: An kammala zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasa a Iran

Dr. Mas’ud Pezeshkian likitan zuciya ne kuma me koyarwa, ya yi aiki a matsayin shugabar Jami’ar Tabriz ta Kimiyyar kiwon lafiya, kuma a halin yanzu memba ne na ma’aikatan ilimi a wannan babbar jami’a a arewacin Iran.

Bayan da ya samu amincewa daga babbar hukumar da ke sa ido kan zabukan kasar na ya tsaya takara a zaben na ranar 28 ga watan Yuni a watan da ya gabata. Ya gabatar da tsare-tsarensa, inda ya jaddada muhimmancin damka ayyuka ga kwararru kuma masu ilimi a gwamnatinsa.

Haka nan kuma ya bayyana Javad Zarif, tsohon ministan harkokin wajen kasar Iran a matsayin zabinsa na shugabancin ma’aikatar harkokin wajen kasar, yayin da ya sha alwashin aiwatar da umarnin Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.

Pezeshkian a hukumance ya shiga takarar neman kujerar shugaban kasar a ranar 1 ga watan Yuni, rana ta uku ta rajista, a ma’aikatar harkokin cikin gida da ke Tehran, tare da rakiyar gungun magoya bayanta.

A muhawarar zagaye na biyu na zaben shugaban kasa, Pezeshkian ya bayyana mahimmancin kiyayewa da cika alkawura a matsayin wani muhimmin al’amari na kiyaye kyawawan halaye.

Ya jaddada muhimmancin nuna girmamawa ga daidaikun mutane, tabbatar da jin muryoyinsu, da bayar da shawarwari kan ayyuka bisa ka’idojin adalci da adalci.

Tsohon ministan lafiya ya kuma jaddada muhimmiyar rawar da amana ke takawa wajen ciyar da al’umma gaba, tare da jaddada cewa gaskiya na da matukar muhimmanci wajen samar da amana a tsakanin al’umma.

Pezeshkian ya jaddada muhimmancin ba da fifiko kan dangantaka da kasashen dake makwabtaka da ita, da fadada huldar dake tsakanin kasashen duniya don bunkasa ci gaban kasar.

A lokuta da dama, ya nanata kudurinsa na mutunta tsarin dokokin Jamhuriyar Musulunci da kuma manufofin da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamene ya bayyana.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Hezbollah ta harba rokoki 200 da jirage marasa matuƙa cikin Isra’ila

Published

on

Hezbollah ta harba rokoki 200 da jirage marasa matuƙa cikin Isra'ila

Hezbollah ta harba rokoki 200 da jirage marasa matuƙa cikin Isra’ila

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ƙungiyar Hezbollah mai da ke Lebanon ta ƙaddamar da hare-haren rokoki fiye da 200 da jirage marasa matuƙa zuwa arewacin Isra’ila, a wani martani na kisan ɗaya daga cikin manyan kwamandojinta.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce an kashe sojanta da dama a hare-haren, na Hezbollah.

Sojojin na Isra’ila sun kuma ce sun mayar da martani kan mayaƙan ƙungiyar da sansanoninta da ke kudancin Lebanon.

Kafofin yaɗa labaran Lebanon sun ce mutum guda ya mutu a wani harin jirgi maras matuƙi da Isra’ila ta kai garin Houla.

Hare-haren na baya-bayan nan, sun kasance mafiya muni cikin watanni tara tsakanin kan iyakokin ƙasashen biyu.

KU KUMA KARANTA: Gaza ya zama gidan marayu kuma maƙabartar yara mafi girma a duniya – Emine Erdogan

An kashe ɗaya daga cikin kwamandojin Hezbollaha wani hari ta sama da Isra’ila ta kai birnin Tyre na ƙasar Lebanon.

Mohammed Nimah Nasser, ya kasance ɗaya daga cikin manyan jagororin ƙungiyar, kafin kisan nasa.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Wani jirgin ruwa ya kife da ‘yan ci-rani a tekun Mauritania

Published

on

Wani jirgin ruwa ya kife da 'yan ci-rani a tekun Mauritania

Wani jirgin ruwa ya kife da ‘yan ci-rani a tekun Mauritania

‘Yan ci-rani kimanin 90 ne suka rasu a kan hanyarsu ta zuwa Turai a lokacin da jirgin ruwan da suke ciki ya kife a farkon makon nan a gabar tekun Mauritania, in ji kafar watsa labarai ta ƙasar wadda ta ambato jami’ai na bayani a ranar Alhamis.

Ana kuma ci gaba da neman da dama da suka bata.

“Jami’an tsaron teku na Mauritania sun gano gawawwakin mutane 89 da suka hau wani babban jirgin ruwan masunta da ya kife a ranar Litinin 1 ga Yuli a gabar tekun Atlantika,” kusan nisan kilomita huɗu daga gabar garin Ndiago a kudu maso-yammacin kasar, in ji kamfanin dillancin labarai na Mauritania a ranar Alhamis.

Jami’an tsaron iyakokin tekun sun kuma kuɓutar da wasu mutanen tara, ciki har da wata yarinya ‘yar shekara biyar, in ji kafar yaɗa labaran.

Kamfanin dillancin labaran ya rawaito cewa wadanda suka kuɓuta na cewa jirgin nasu ya taso ne daga iyakar Senegal da Gambia dauke da fasinja 170, wanda hakan ya sanya ake neman mutane 72 da suka ɓata.

Wani babban jami’in karamar hukuma a yankin da ya nemi a boye sunansa ya tabbatar wa AFP aukuwar lamarin.

KU KUMA KARANTA: Jirgin sojin Najeriya ya faɗo a Kaduna

Hanyar tekun Atlantika na da hatsari sosai saboda manyan igiyar ruwa, kuma ‘yan ci-rani na yin lodin da ya haura ka’ida a jiragen ruwa, a mafi yawan lokuta jiragen ba su da ingancin shiga teku, kuma ba sa ɗaukar isassen ruwan sha.

Amma hakan ya sake fitowa fili ne sakamakon yadda ake ƙara sanya idanu kan tekun Bahar Rum.

A shekarar 2023 adadin ‘yan ci-rani da suke zuwa tsibiran Canary na Sifaniya ya ninka a shekara guda, wanda ya kai mutane 39,910, kamar yadda gwamnatin Sifaniya ta bayyana.

Tsibiran Canary na Sifaniya na daura da iyakar tekun arewacin Afirka da nisan kilomita 100.

Amma jiragen ruwa da dama – mafi yawansu na katako – na kama hanya daga Maroko, Yammacin Sahara, Mauritania, Gambia da Senegal don zuwa tsibiran na Sifaniya.

Sama da ‘yan ci-rani 5,000 ne suka mutu a teku yayin ƙoƙarin tsallaka wa Sifaniya a watanni biyar na farkon wannan shekarar, kenan mutane 33 ne ke mutuwa kowacce rana, kamar yadda Caminando Fronteras, wata ƙungiyar bayar da agaji ta Sifaniya ta bayyana.

Wannan ne adadin rasa rayuka mafi yawa tun bayan da kungiyar ta fara tattara bayanai a 2007, kuma mafi yawa na mutuwa ne a hanyar tekun Atlantika.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like