Najeriya ta gano ‘haramtattun’ matatun man fetur 50 a yankin Neja Delta

0
176

Hukumomi a Najeriya a ranar Lahadi sun ce sun gano wasu haramtattun wurare 50 da ake aikin tace man fetur ba bisa ƙa’ida ba.

Rear Adm. John Okeke, kakakin rundunar ‘Operation Safe Delta’ da take aiki a yankin Neja Delta mai arzikin man fetur na kasar, ya ce sojoji na ci gaba da kai hare-hare kan masu fasa kwabrin mai a yankin.

Okeke ya lura cewa an kama man fetur mai yawa sosai da aka sace.

Ƙaruwar satar man fetur da ake yi a Najeriya na yin illa ga tattalin arzikin kasar.

KU KUMA KARANTA: Rikicin Isra’ila da Iran ne ya haddasa matsalar man fetur a Najeriya — IPMAN

Wani ɗan majalisar dattijan ƙasar, Sanata Ned Nwoko a baya ya taɓ bayyana cewa kasar ta yi asarar sama da dala biliyan uku a shekarar 2023 sakamakon ƙaruwar satar mai da hare-hare kan bututan mai.

Arzikin man fetur da Najeriya ke da shi ya kai kusan ganga biliyan 37, wanda ya zama kashi 3.1% na yawan wanda ake adane da shi a duniya.

A matsayinta na daya daga cikin kasashe 15 masu arzikin ɗanyen mai a duniya, Najeriya tana matsayi na takwas a fannin arzikin man da aka tabbatar, sannan ta shida wajen fitar da mai.

Yankin na Delta, inda ake da rijiyoyin mai, yana fama da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da ke yin zagon ƙasa a rijiyoyin mai, lamarin da ke haifar da rigingimu da garkuwa da mutane da sauran tashe-tashen hankula a yankin.

Leave a Reply