Najeriya ta ce ba ta ji daɗin ficewar Nijar, Mali da Burkina Faso daga ECOWAS ba

0
132

Najeriya ta bayyana rashin jin daɗinta kan sanarwar da gwamnatin mulkin sojin Nijar ta yi wacce ke nuna cewa ƙasashen Burkina Faso da Mali da kuma Nijar din sun janye daga kasancewarsu a Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS.

Sanarwar ta Najeriya na zuwa ne a ranar Litinin, a lokacin da jama’a da dama a faɗin yankin ke ta tofa albarkacin bakinsu kan batun, tun bayan da ƙasashen uku suka sanar da matakin nasu a ranar Lahadi da hantsi.

Ƙasashen sun ce sun ɗauki matakin ficewa daga ECOWAS ne saboda ta gaza taimaka musu wurin shawo kan rashin tsaron da ke addabar su da ma sauran ƙalubalen da suke fama da su.

Amma tun da fari ECOWAS ta ce har yanzu a hukumance ƙasashen Mali, Burkina Faso da Nijar ba su sanar da ita matakinsu na fita daga cikinta ba.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya wacce ta fitar da sanarwar rashin jin daɗin ƙasar kan matakin makwabtan nata, ta ce “Kusan shekara 50 kenan ECOWAS take aiki don wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da dimokuraɗiyya a yankin.

“Najeriya tana tare da ECOWAS don jaddada tsarin da ya dace da kuma ƙudurinmu na kare da ƙarfafa hakki da jin daɗin dukkan ‘yan ƙasashe mambobin ƙungiyar,” in ji sanarwar mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun ma’aikatar, Ambasada Francisca Omayuli.

KU KUMA KARANTA: Har yanzu ba mu samu labarin fitar Nijar, Mali da Burkina Faso daga cikinmu ba – ECOWAS

Ta ci gaba da cewa Najeriya ta yi aiki da gaskiya da aminci wajen tuntuɓar dukkan ‘yan’uwa na ƙungiyar ECOWAS don magance matsalolin da muke fuskanta. Yanzu a bayyane yake cewa waɗanda ke neman barin al’ummarmu ba su da irin wannan kyakkyawar aniya.

“Maimakon haka, shugabannin da ba zaɓaɓɓu ba, suna hana jama’arsu ‘yancin yin zaɓi na asali game da ‘yancin yin tafiya da ‘yancin yin kasuwanci da ƴancin zaɓar shugabanninsu.”

Sai dai Najeriya ta ce kofarta a buɗe take don tattaunawa da Burkina Faso da Mali da Nijar ta yadda al’ummomin yankin za su ci gaba da jin daɗi da cin moriyar tattalin arziki da ƙimar dimokuraɗiyya da ƙungiyar ECOWAS ta amince da su.

Ta kuma yi ƙira ga ƙasashen duniya da zu ci gaba da ba da goyon bayansu ga ECOWAS da kuma haɗin kai.

Leave a Reply