Najeriya ta ƙara shiga yanayin ƙarin haraji bayan cire tallafin Fetur

Masana sun bayyana cewa, jan ragama da akalar rayuwar talakan ƙasa ya ta’allaƙa ne a wuyan gwamnati ta kowane fanni kama daga samar da ilimi, lafiya, tsaro da kuma abun dogaro da kai.

Bisa tsari irin na gwamnati, gwamnati ne ya kamata ta jajirce wajen tabbatar da cewa, talakan ƙasa ya samu duk wasu abubuwan more rayuwa da kuma walwala.

Ƙarancin Man Fetur
Sai dai a Najeriya tun daga lokacin da aka cire tallafin man fetur tsadar rayuwa ta ke ƙara ta’azzara. Haka kuma ɗimbim harajin da gwamnatin ke ɗorawa al’ummar ƙasar ya zamo tamkar talaka ne ke ɗaukar nauyin gwamnatin.

KU KUMA KARANTA:Mutane 13 sun mutu, 27 sun ɓace, sakamakon nutsewar wani jirgin ruwa a gaɓar tekun Tunisiya

A hirar shi da Muryar Amurka, ‘Mukhtar Muri da ke kantin kwari a jihar kano ya bayyana cewa, ‘yan kasuwa na fuskantar barazana kan harajin da a ke yawan karɓa a wajen su.

A nashi bayanin, mai sharhi kan tattalin arziki Abubakar Ali ya ce, “Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu yana so ya yi amfani da salon samar da kuɗaɗen shiga kamar yadda ya yi a lokacin da ya ke Gwamnan jihar Legas, amma bai yi la’akari da halin da ƙasar, da kuma al’ummar ƙasar ke ciki a yanzu ba.”

A jawabinsa game da yawan harajin, Ministan yaɗa labaru Muhammad Idris ya ce, “gwamnati za ta duba tsarin biyan harajin domin al’ummar ƙasar su samu sauƙi.”

Hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta yi hasashen cewa, kuɗaɗen shiga zai ƙaru da kashi 57 cikin ɗari a shekarar 2024 zuwa Naira tiriliyan 19.4 idan aka kwatanta da bara.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *