Najeriya na kan tsini – Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar

0
124

Mai alfarma sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III ya bayyan fargabar cewa Najeriya na fuskantar barazanar tsaro bisa la’akari da yadda ɗumbin matasan ƙasar ke fama da rashin aikin yi da yunwa.

Sarkin Musulmin ya yi waɗannan kalamai ne yayin da yake jawabi a wani taron majalisar sarakunan gargajiya ta arewacin Najeriya ranar Laraba a Kaduna.

Muhammad Sa’ad Abubaakr III ya ce ” mun shiga wani sabon zango na shugabanci. An samu sabbin gwamnoni inda kuma wasu suka yi tazarce a karo na biyu amma har yanzu muna fama da matsalar tsaro.

KU KUMA KARANTA: Yara biliyan 1.4 ne suke rayuwa cikin matsanancin talauci a duniya — MƊD

Babban matsalar ma ita ce ƙaruwar talauci. Mafi yawancin mutanenmu ba su da hanyoyin samun abin da za su ci su sha”.

Ya ƙara da cewa idan dai har gwamnoni na son zaman lafiya a jihohinsu, dole ne su sama wa matasa aikin yi sannan dole ne su yi aiki tare da sarakunan gargajiya.

“Dole ne mu sama wa ɗimbim matasanmu masu zaman kashe wando ayyukan yi. Na sha faɗar cewa muna wasa da bakin wuta. Saboda samun miliyoyin matasa ba tare da ayyukan yi ba sannan suna fama da yunwa, hakan na nufin muna fuskantar barazana.”

Daga ƙarshe ya ce ya yi amannar cewa za a samu mafita duk da cewa “Najeriya ba ta taɓa gaza samar da mafita ba illa dai kawai ba a iya aiwatarwa”.

Leave a Reply