Najeriya na cikin ƙasashen da yawan al’ummarta zai yi ta ƙaruwa – MƊD 

0
85
Najeriya na cikin ƙasashen da yawan al'ummarta zai yi ta ƙaruwa - MƊD 

Najeriya na cikin ƙasashen da yawan al’ummarta zai yi ta ƙaruwa – MƊD

Hukumar Kidayar Yawan Al’umma na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNFPA) ta ce tuni yawan jama’ar duniya da ke ci gaba da ƙaruwa a sassa da yankuna daban-daban tuni ya zarce mutane biliyan takwas.

UNFPA ta ce ƙasashe irin su Najeriya a yankin Afirka, na daga cikin waɗanda yawan jama’rsu zai yi ta ƙaruwa nan da shekaru masu zuwa.

A cewar sabon rahoton na UNFPA kan yawan jama’a na 2024, sauye-sauyen yawan al’ummar duniya ya nuna gagarumin sauye-sauyen da ake samu a yanayin ci gaban yanki da yawan jama’a da kuma yawan birane.

Rahoton ya ce mutane ‘yan shekaru 65 zuwa sama sun kusan ninka sau biyu zuwa kashi 10.3%, kuma ana sa ran wannan yanayin zai ci gaba.

Yayin da jama’a ke ƙara tsufa a duniya, yankunan Turai da Arewacin Amurka, da sassan Asiya suna ganin ƙaruwar yawan tsofaffi, lamarin da ke haifar da ƙalubale ga kiwon lafiya da shirye-shiryen ritaya da haɓakar ayyuka.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware duk ranar 11 ga watan Yuli a matsayin “Ranar Yawan Jama’a ta Duniya” don faɗakar da jama’a a kan abubuwan da suka shafi yawan al’umma.

Kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya tattara bayanai daga majiyoyin MƊD kan halin da al’ummar duniya ke ciki a halin yanzu, da suka hada da ci gaban yankuna da raguwar yanayin da ake ciki, albarkacin ranar yawan jama’a ta duniya.

KU KUMA KARANTA: Ƴan gudun hijirar Sudan da ke Chadi na fuskantar tsananin rayuwa shekara guda da soma yaƙi

Afirka ta kasance yankin da ya fi samun saurin bunƙasar jama’a, inda ake sa ran karuwar yawan jama’a a kasashe kamar Najeriya da Habasha da Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo saboda yawan haihuwa da kuma inganta harkokin kiwon lafiya.

Ana kuma samun ƙaruwar jawan jama’a sosai a Gabashi da Kudancin Afirka, mai yawan jama’a miliyan 688, da kuma a Yammacin Afirka da Tsakiyar Afirka, mai yawan mutane miliyan 516.

A Asiya kuwa, ƙasashe irin su Indiya da China suna samun raguwar yawan jama’a saboda raguwar yawan haihuwa, yayin da ƙasashen kudu maso gabashin Asiya irin su Indonesia da Philippines ke ci gaba da samun matsakaicin ci gaba.

A Turai, ƙarancin yawan haihuwa da yawan tsufa da yanayin ƙaura suna haifar da raguwar yawan jama’a.

Ƙasashe kamar Jamus da Italiya da Rasha suna fuskantar ƙalubale tare da raguwar ma’aikata da hauhawar dogaro.

Bisa ƙididdigar da UNFPA ta fitar, yawan mutanen duniya masu shekaru 65 zuwa sama ya kusan ninka sau biyu daga kashi 5.5% a shekarar 1974, zuwa kashi 10.3 cikin 100 a shekarar 2024.

An yi hasashen wannan adadi zai kai kashi 20.7% nan da shekarar 2074, sannan adadin ‘yan shekara 80 zuwa sama sai nunka sau uku.

A halin yanzu ƙasashen da suka ci gaba ne ke da kaso mafi tsoka na yawan tsofaffi, yayin da kasashe masu tasowa galibi ke da mutanen da shekarunsu ke haurawa.

Samun yawan tsofaffi a duniya yana da alaƙa da ƙaruwar matsakaicin tsawon rayuwa da raguwar yawan haihuwa a ƙasashe da yawa.

Leave a Reply