Kongo ta jaddada kasancewarta mamba a ƙungiyar Organization of Petroleum Exporting Countries (OPEC) ta ƙasashe masu arzikin man fetur, kwanaki kaɗan bayan makwabciyarta Angola ta yanke shawarar fita daga ƙungiyar.
“Jamhuriyar Kongo tana jaddada goyon bayanta game da tsare-tsare da manufofin Sakatare Janar na OPEC da kuma OPEC+,” a cewar wata sanarwa da ministan makamashin ƙasar Bruno Jean-Richard Itoua ya wallafa a shafinsa na LinkedIn ranar Asabar.
“Kongo za ta ci gaba da hada kai na kut da kut da dukkan mambobin ƙungiyar.”
KU KUMA KARANTA: Ana tsananin buƙatar man fetur a Gaza, saboda ayyukan asibitoci — MƊD
Hakan na faruwa ne bayan Najeriya ta jaddada zamanta a ƙungiyar OPEC inda ƙaramin ministan man fetur Heineken Lokpobiri ya ce ƙasarsa ba za ta gaza wajen ci-gaban ƙungiyar ba.
“Haɗin kanmu da ƙungiyar shi ne yake samar da zaman lafiya da ɗorewar cinikayya a kasuwar man fetur,” in ji Lokpobiri a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
“Muna tsaye tsayin-daka wajen ganin OPEC ta cim ma muradunta inda za mu ci gaba da hada gwiwa wajen kawar da duk wani ƙalubale da ya shafi ƙasarmu da ma nahiyarmu baƙi ɗaya.”
An bai wa Kongo, wadda ta zama cikakkiyar mamba ta OPEC a 2018, damar fitar da ganga 277,000 ta ɗanyen fetur a kullum zuwa 2024, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Najeriya, wadda ita ce kasa mafi girma da ke hako ɗanyen fetur a Afirka, da Angola suna cikin ƙasashe da dama da aka bai wa damar fitar da ɗanyen fetur ƙasa da wadda aka bai wa Kongo zuwa 2024 saboda sun gaza cika alkawuran da suka ɗauka a baya.
Ranar Alhamis Ministan Fetur na Angola Diamantino Azevedo ya ce OPEC ba ta yi wa ƙasarsa adalci ba.
Hakan ne ya sa ƙasarsa ta bi sahun ƙasashe irin su Ecuador da Qatar wurin fita daga ƙungiyar a shekaru goma da suka gabata.