Uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, ta ce ba za a ayyana Najeriya a matsayin matalauciyar ƙasa ba duk da irin matsalolin da ta ke fuskanta.
Sai dai ta yi ƙira ga masu hannu da shuni da su taimaka wa talakawa. .
A sakonta na Kirsimeti a gidan marayu na Nana Berry da ke Abuja, ta ce 2024 za ta zama shekara mai cike da alfahari ga ‘yan Najeriya.
Ta ce, “Yayin da muke shiga shekara ta 2024, ya kamata sakonmu ya zama yadda zai sauya rayuwar matasa.
“Ya kamata mu daina maganar talauci a gaban ’ya’yanmu, mu ba talakawa ba ne, masu hannu da shuni su ma su kula da talakawa su taimake su, shi ke nan abin da ake buƙata.
KU KUMA KARANTA: NSCDC ta girke jami’ai 780 a Gombe saboda bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara
“Mun cire batun talauci daga cikin al’amuranmu saboda yana gurɓata zukatan matasa. Za mu shiga shekara mai cike da fata nagari.”
Uwargidan shugaban ƙasar ta shawarci iyaye da su rungumi ɗabi’ar koyar da yaransu kyawawan dabi’u don su zama manya nagari.