NAHCON za ta haramta amfani da dala a aikin hajji, don rage tsadar kuɗin kujera

0
25
NAHCON za ta haramta amfani da dala a aikin hajji, don rage tsadar kuɗin kujera

NAHCON za ta haramta amfani da dala a aikin hajji, don rage tsadar kuɗin kujera

Ya kuma jaddada cewa shawo kan wannan matsala zai samar da gagarumin rangwame a farashin kujerar aikin Hajjin 2025.

Hukumar Alhazan Najeriya (NAHCON) ta sanar da shirinta na haramta amfani da takardar kudin dala wajen biyan kudaden aikin hajji, matakin da aka tsara da nufin rage tashin gwauron zabon da kudin kujerar aikin hajji ke yi.

Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ne ya bayyana hakan sa’ilin da ya ziyarci fadar mai martaba Sarkin Argungu.

KU KUMA KARANTA:Mun gano yadda ake amfani da sunan mu a nemi kwangilar kama masauƙai da abinci a Saudia — NAHCON

Shugaban na NAHCON ya kara da cewa biyan muhimman lamuran aikin hajji, irinsu kudin jirgi da dala ya yi matukar taimakawa wajen tsadar aikin hajjin, abin da ya sanya ‘yan Najeriya da dama ba za su iya biya ba.

Saleh ya ci gaba da cewa a yayin da maniyata ke biyan kudin Umrah da Naira, kamfanonin jiragen sama da sauran masu ruwa da tsaki kan dage a kan biyan kudin aikin Hajji da dala, inda suke haifarwa maniyata da cikas babu gaira ba dalili.

Ya kuma jaddada cewa shawo kan wannan matsala zai samar da gagarumin rangwame a farashin kujerar aikin Hajjin 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here