NAHCON ta ƙaryata rahotanni kan ƙin fitar Alhazan Najeriya da dama daga Saudiyya

0
64
NAHCON ta ƙaryata rahotanni kan ƙin fitar alhazan Najeriya da dama daga Saudiyya

NAHCON ta ƙaryata rahotanni kan ƙin fitar Alhazan Najeriya da dama daga Saudiyya

Hukumar Alhazana Najeriya (NAHCON) ta ƙaryata rahotannin da ke cewa fiye da ’yan ƙasar 600 ne suka ƙi komawa gida bayan sun kammala Umrah a ƙasar Saudiyya.

Martanin na Hukumar Alhazai (NAHCON) na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya yi zargin cewa fiye da ‘yan Najeriya 600 da suka je Umrah a Saudiyya sun ƙin komawa gida.

Shehu Sani ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, inda ya ce ”fiye da ‘yan Najeriya 600 ne da suka isa Saudiyya don aikin Umrah suka ƙi komawa gida.”

Ya ƙara da cewa,”lamarin zai tilasta wa hukumomin Saudiyya ɗaukar tsauraran matakai wajen bayar da biza, kana da yawa daga ‘yan Najeriya da suke son zuwa yanzu ba za su samu da dama ba.”

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Neja bai yi mana adalci ba – Hukumar Alhazai

Sai dai Mataimakiyar Daraktan Hulɗa da Jama’a ta NAHCON, Fatima Usara, ta musanta wannan iƙirarin, inda ta ce hukumomin Saudiyya ko na Najeriya ba su da wannan labari ballantana ta tabbatar da shi.

“Ba mu tattaro wani labari mai kama da wannan ba ko kuma daga Saudiyya ba, kazalika Ma’aikatar Harkokin Waje da kuma na Shiga da Fita da ƙasashen biyu ba su bayyana mana wannan labari ba,” kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika Hausa.

Ko da yake dai iƙirarin Sanata Shehu Sani na zuwa ne kusan wata biyu da kammala aikin Hajjin bana, kana kwanaki kaɗan da Shugaba Bola Tinubu ya sauƙe shugaban hukumar NAHCON, Jalal Arabi, bisa zargin almundahana da karkatar da maƙudan kudaɗe na tallafin Hajji da gwamnati ta bayar.

Sama da alhazai 50,000 ne daga Najeriya suka je aikin Hajjin 2024 bayan kowanne ya biya kusan Naira miliyan 7.

Sai dai Fatima Usara ta ce, duka alhazan sun koma gida Najeriya cikin ƙoshin lafiya, in ban da mutum ɗaya wanda ba a gan shi ba tun daga ranar farko da ya sauka a Saudiyya har ya zuwa lokacin da aka bar ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here