Nafisa ta cancaci shugaba Tinubu ya yi mata kyautar dala dubu 100, gida da OON — Pantami

0
186
Nafisa ta cancaci shugaba Tinubu ya yi mata kyautar dala dubu 100, gida da OON — Pantami
Ɗaliba Nafisa da Farfesa Pantami

Nafisa ta cancaci shugaba Tinubu ya yi mata kyautar dala dubu 100, gida da OON — Pantami

Daga Jameel Lawan Yakasai

Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ba wa ɗalibar nan ’yar shekara 17 daga Jihar Yobe da ta lashe Gasar Turanci ta Duniya, Nafisa Abdullah Aminu, kyautar tsabar kuɗi Dala 100,000 da gida da kuma lambar girmamawa ta OON.

Farfesan ya buƙaci a gayyato Nafisa da malamanta na harshen Turanci musamman zuwa Fadar Shugaban Ƙasa a karrama su saboda yadda suka ɗaga sunan Najeriya a idon duniya a fannin ilimi.

“Ina kira da babbar murya cewa a a ba wa Nafisa kyautar tsabar kuɗi Dala 100,000 da gida da kuma lambar girmamawa daga Gwamnatin Tarayya.”

A cikin saƙon da ya wallafa a safiyar Talata, Pantami ya ƙara da cewa malaman Nafisa sun cancanci irin kyautar da aka yi wa tawagar masu horas da ’yan wasan Najeriya ta lambar OON da tsabar kuɗi Dala 50,0000 da kuma gida ga kowannensu, musamman ma tun da nasarar da suka samu a fannin ilimi ne.

KU KUMA KARANTA: ‘Yar jihar Yobe ta lashe gasar Turanci ta Duniya a Burtaniya

“Su ma malananta a ba su kyauta irin wadda aka yi wa masu horas da ’yan wasan ƙwallon Najeriya. Wajibi ne mu ba wa ilimi muhimmancin da ya dace tare da karrama ƙwazon ’yan kasarmu,” a cewar Pantami.

Bayanin na zuwa ne washegarin da Gwamnatin Tarayya ta yi irin wannan kyauta ga kowacce daga ’yan wasan ƙwallon kwandon Najeriya na D’Tigress kan lashe gasar Kaifin Nahiyar Afirka ta shekarar 2025.

Ƙasa da mako guda ke nan kuma bayan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi irin wannan kyauta ga ’yan wasan ƙwallon ƙafan mata ta Super Falcons bayan sun lashe gasar Kofin Nahiyar Afirka ta bana.

Jaridar Neptune Prime ta ruwaito cewar Nafisa Abdullah Aminu ta lashe Gasar Turanci ta Duniya ta Teen Eagle da aka gudanar a ƙasar Birtaniya.

Nafisa daga Kwalejin Nigeria Tulip International (NTIC) da ke Jihar Yobe ta doke abokan fafatawarta daga ƙasashe 69 domin zama Gwarzuwar Shekarar 2025.

Leave a Reply